Ofishin Jakadancin Kasar Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da bikin cikar ranar kasa ta Saudiyya karo 93 a gidan Ambasadanta da ke Abuja, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da shugabannin ofisoshin diflomasiyya da kungiyoyin kasa da kasa da kuma ‘yan kasuwa da sauran manyan mutane.
A nasa jawabin, Jakadan Kasar Saudiyya a Nijeriya H.E. Faisal bin Ebraheem Alghamdi ya bayyana cewa, Masarautar tana bikin cika shekaru 93 na hadin kan sassan Masarautar Sarki Abdulaziz bin Abdulrahman Al Saud (Allah Ya jikansa) a karkashin wata kungiya mai karfi wacce aka kafa ta bisa akidar Musulunci wacce daidaito, adalci da amana suka tabbata a cikinta.
- A Shirye Sin Take Ta Inganta Hadin Gwiwa Da UNESCO Domin Samar Da Ci Gaba Da Zaman Lafiya A Duniya
- Manyan Batutuwa 7 Da Za Su Turnike Zauren Majalisa Bayan Dawowa Hutu
Alghamdi ya kuma bayyana cewa, akwai kyakkyawar alaka a tsakanin Masarautar da Nijeriya mai cike da tarihi wacce ta ke ta ci gaba da bunkasa tun lokacin da aka kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu a shekarar 1961. Ya kuma yi fatan alheri da nasara ga mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake tsokaci kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, jakadan ya ce, sama da mahajjata ‘yan Nijeriya 200,000 da masu zuwa (Umara) da maziyarta sun ziyarci Masarautar a shekarar da ta gabata, kuma Masarautar ta bai wa daliban Nijeriya tallafin karatu sama da 200 don yin karatu a jami’o’in kasar daban-daban. Ya kara da cewa, yawan cinikin da ke tsakanin kasashen biyu ya haura Dala miliyan 600.
A kan taimakon jin kai ga al’ummar Nijeriya. Jakadan Masarautar ya bayyana cewa, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud (Allah Ya kare shi) ya ba da umarnin aiwatar da taimakon sa-kai na Nur-Saudi a Nijeriya, wanda aka fara aiwatarwa mataki-mataki; An aiwatar da matakin farko wanda aka nufi yakar makanta da musabbabanta, sannan kuma ta yi wasu ayyukan tiyata musamman a bangaren mafitsara da raba tagwayen da aka haifa a Jone.
Jakadan ya taya iyayen tagwayen murna da aka yi nasarar raba su a watan Mayun da ya gabata, a aikin tiyata mai lamba 56 da masarautar ta yi wajen raba wasu tagwaye daga sassan duniya.
A karshe, jakadan ya mika godiya ga kasashen duniya da abokan arziki daga ciki har da tarayyar Nijeriya bisa goyon bayan da ta bai wa Saudiyya na karbar bakuncin bikin baje kolin duniya na 2030 a birnin Riyadh, wanda ya zo daidai da ranar da Saudiyya ta ke shirin kaddamar da kudirinta na shekarar 2030.