Tsohon dan majalisar dattawa daga Jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa muddin kwamitin binciken majalisar dokokin Jihar Kaduna da gaske take kan badakalar bashin da tsohuwar gwamnatin jihar ta ciwo, sai an gayyato tsohon gwamna jihar, Nasiru el-Rufai wanda shi ne kadai zai iya bayyana yadda ya yi da dukiyar al’umma.
Sanata Shehu Sani ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a sakatariyar ‘yan jaridu da ke Jihar Kaduna jim kadan bayan kammala taron tunawa da zagayowar ranar haihuwar wakilin jaridar “The Guardian” na Jihar Kaduna Mista Sadon.
- Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna
Shehu Sani, ya ce idan da shi ne gwamna Jihar Kaduna da tuni ya gurfanar da duk wani wanda ake zargin ya wawure dukiyar al’ummar jihar. Ya shawarci kwamitin binciken majalisar dokokin jihar da ya gaggauta gayyato el-Rufai domin yi masa bayanin yadda aka salwantar da makudan kudadan al’ummar jihar.
Ya kara da cewa kwato kudin rancen da bankin duniya ya bayar na dala miliyan 350 da wasu jami’an tsohuwar gwamnatin Kaduna suka wawure ba za a iya samu ba ta hanyar gayyata da yi wa tsofaffin kwamishinoni da masu ba da shawara tambayoyi ba tare da gayyato tsohon gwamna da kuma yi masa tambayoyi ba.
Tsohon sanatan ya ce el-Rufai shi ne kadai zai iya amsa tambayoyi kan bashin tare da bayyana inda aka dawo da kason Kaduna na Paris, Edcess Crude Funds, Stamp Duties Funds, Ecological Funds da billiyoyin kudin lamunin da aka karba daga babban bankin duniya da bankunan cikin gida.