ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Binciken CGTN: Sama Da Kashi 80% Na Masu Amsa Tambayoyi A Duniya Sun Yaba Da Manufar Harkokin Waje Na Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
CGTN

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Kwanan baya, tashar talabijin ta kasa da kasa ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta hada kai tare da jami’ar Renmin ta kasar don fitar da wani binciken jin ra’ayin jama’ar duniya ta hanyar cibiyar nazarin sadarwa ta kasa da kasa ta sabon zamani, wato New Era International Communication Research Institute, inda aka nuna cewa, sama da kashi 80% na wadanda suka amsa tambayoyin binciken a duniya sun yaba da manufar harkokin wajen kasar Sin mai lumana kuma mai cin gashin kanta, a ganin su, hakan zai taimaka wajen samar da tsarin kasa da kasa mai adalci yadda ya kamata.

An gudanar da binciken ne a tsakanin mutane 31,980 a duniya, ciki har da na kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Jamus, Faransa, da Japan da sauransu, da kuma na kasashe masu tasowa irin su Mexico, Thailand, da Najeriya da dai sauransu.

  • Xi Ya Jaddada Zurfafa Gyare-gyare Don Inganta Kwarewa A Sabbin Fannoni
  • Sin Da Aljeriya Na Fatan Bunkasa Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki

A cikin wadanda suka ba da amsa, 91.1% daga cikinsu sun nuna yabo sosai game da jerin nasarorin da aka cimma bisa ga shawarar “Ziri daya da hanya daya” a cikin shekaru goma da suka gabata. Kana kashi 82.5% daga cikinsu suna ganin cewa, manufar “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam” ta kara azama mai dorewa ga kafa kyakkyawar makoma ga bil-Adam, tare da nuna madaidaiciyar hanyar da ya kamata dan Adam su bi. Baya ga haka, kashi 84.5% daga cikinsu sun yarda da ainihin manufar shirin ci gaban duniya, kuma sun yi imanin cewa ci gaba shi ne hanyar magance matsalolin kasa da kasa da tabbatar da jin dadin zaman rayuwar jama’a. Kashi 85.6% na masu amsar sun yi imanin cewa, tsaro shi ne muhimmin abun da ake bukata don samun ci gaba, kuma ya kamata kasashe daban daban su yi aiki tare don gina daidaitaccen tsarin tsaro mai inganci da dorewa.

ADVERTISEMENT

Bisa binciken kuma, a ganin kashi 76.2% na masu amsa tambayoyi, manufar harkokin wajen kasar Sin ta kiyaye moriyar kasar yadda ya kamata, kana kashi 65.3% na masu amsa tambayoyin sun yi imanin cewa, yadda kasar Sin ke taka rawa a harkokin duniya ya kawo tabbaci da kwanciyar hankali ga kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
Gwamnan kano

Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar 

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.