Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ya nuna yadda al’ummun kasa da kasa ke nuna rashin jin dadi da jerin matakan gwamnatin Amurka, na dakile samarwa dalibai ‘yan kasashen waje damar yin karatu ko bincike a jami’o’in kasar.
Binciken ya nuna kaso 82.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayin, na matukar adawa da hakan, inda suke zargin Amurka da matukar tauye damar samun ilimi. A daya hannun kusan kaso 90 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na ganin wadannan matakai na gwamnatin Amurka, sun dakile “Mafarkin Amurka”, na samar da dama ga dubban dalibai ‘yan kasashen waje.
- Majalisar Dokokin Katsina Ta Ayyana Gwamna Radda A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A 2027
- Bam Ya Kashe Mutane 9 A Wata Tashar Motoci Da Ke Borno
A baya bayan nan ne dai gwamnatin Amurka, ta umarci ofisoshin jakadancinta da kananan ofisoshin wakilci dake kasashen ketare, da su dakatar da shirin bayar da Biza, tare da duba yiwuwar bincikar shafukan kafofin sada zumunta na daliban waje. Game da hakan, kaso 81.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na adawa da hakan, suna kallon matakin a matsayin kutsawa cikin sirrin daliban, wanda ke cike da tsana da nuna banbanci ga daliban kasashen waje.
Bugu da kari, Amurka ta soke Bizar daliban Sin ta hanyar fakewa da banbance-banbance akida da tsaron kasa, wanda hakan ya haifar da matukar suka daga sassa da dama.
Binciken ya kuma nuna cewa, kaso 83 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin matakin zai illata halastattun hakkoki na daliban kasar Sin, tare da haifar da shinge na rashin adalci, wanda zai katse musaya tsakanin al’ummun kasashen biyu.
Kafar CGTN ta kasar Sin ce ta wallafa binciken jin ra’ayin jama’ar kan dandalolin harsunan turancin Ingilishi, da Sifaniyanci, Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha, inda masu bayyana ra’ayoyi 6,886 daga sassan kasashen ketare daban daban suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp