Shugaban Amurka Joe Biden a ranar Laraba ya rattaba hannu kan dokar ba da tallafin dalar Amurka biliyan 95 ga wasu kasashe, bayan da majalisar kasar ta amince da dokar a daren Talata. A cewar wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ya gudanar ta intanet, kaso 89.87% na masu ba da amsa sun yi imanin cewa, tallafin da Amurka ke bayarwa a ko da yaushe, ya kasance yana inganta muradun Amurka ne tun daga farko har karshe, tare da yin watsi da muradun ci gaba na dogon lokaci na kasashe maso tasowa masu karbar tallafin.
Ban da haka kuma, kusan kaso 94.92 na masu ba da amsa sun yi imanin cewa, tallafin Amurka na da alaka da muradun dilolin makamai, kuma Amurka na samun ribar yaki ta hanyar rikicin bil Adama. Kaso 89.34 na masu ba da amsa sun damu cewa, taimakon aikin soja da Amurka ke baiwa kasashe ko yankunan da ke fama da rikici zai kara dagula rikicin yankuna. (Yahaya)