Rahoton matsayar kasar Japan kan tsaro na shekarar 2025 na ci gaba da haifar da damuwa game da abin da ta kira da “tsaro”. Yayin da batun ya zo da wani sabon abu, burin da ake da shi na fadada shi ya kara haifar da damuwa da rashin amincewa da matsayin da Japan ta dauka a kan tsaro.
Wani binciken jin ra’ayin jama’a na duniya da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 82.6 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyi sun yi nuni da cewa da gangan kasar Japan ta kirkiri batun barazana daga waje don tabbatar da fadada sha’anin sojojinta, matakin da zai yi matukar kawo cin amana tsakanin kasashen Asiya da ma kasashen duniya.
A hakikanin gaskiya, wadda ke ci gaba da rura wutar barazanar tsaro a yankin arewa maso gabashin Asiya da ma fadin Asiya da tekun Fasifik ba kowa ba ce illa Japan da kanta. Bisa yadda kasafin kudinta na tsaro na FY2025 ya kai adadin kudin kasar yen tiriliyan 8.7, kashi 76.2 cikin 100 na masu amsa tambayoyi sun yi imanin cewa gwamnatin Japan ta saba wa tsarin mulkinta na samar da zaman lafiya da alkawurran da ta daukarwa duniya bayan yaki.
Binciken jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a dukkan dandalolin kafar CGTN na Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci da Rashanci, ya tattaro amsoshi daga masu bayyana ra’ayoyi 5,365 cikin sa’o’i 24. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp