Hassan Hussaini Liman, Sadiq usman
Hankulan al’umma sun yi matukar tashi a wannan makon sakamakon rahotannin mutuwar wasu iyalai a sassa daban-daban na kasar nan musamman Arewa a sanadiyyar cin gurbataccen abinci.
Mace-macen iyalan wadanda suka auku a Jihohin Kano, Sakkwato, Zamfara da sauransu, sun rutsa da iyaye da ‘ya`yansu a lokuta daban-daban.
Asalin Abin da ya faru a Kano
Bayan bayyanar labarin wata uwa da aka ce ta rasu tare da ‘ya`yanta biyar bayan sun ci “danwake” a kauyen Karkari da ke Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, wakiliyarmu ta yi tattaki zuwa kauyen domin binciko asalin abin da ya faru, inda sakamakon bincikenta ya gano cewa ba yadda aka yada labarin haka al’amarin ya kasance ba.
An ce uwar, Alhakatu Abdulkarim da ‘ya’yanta biyar Bashir Abdulkarim da Firdausi da Hafsat da Usman da Jamilu, sun rasu ne saboda garin da aka hada “danwaken” da shi ya riga ya lalace. Sai dai kuma bincikenmu ya gano, Gauda ce uwar ta girka ba danwake ba, wadda ta yi amfani da dussa da gari wajen hadawa. Shi ma ba wannan ne ya yi ajalinsu ba.
Ga yadda al’amarin ya faru dalla-dalla.
Bayanin kanin mijin matar, Malam Yahaya Dantsoho
“Abin da ta yi wajen hada abincin shi ne, ta yi Gauda a wannan rana ta ga garinta ba zai isa ba sai ta debo wannan dusa ta daka sai hada ta yi abinci. A ranar Talata (ta makon jiya) da safe, marigayiyar ta zo wurina tana cewa danta karamin ya yi amai ba shi da lafiya, don haka ta yanke shawarar za ta kai shi asibitin koyarwa na makotanmu, sai na ce a kirawo dan kishiyarta babban, sai ta ce to, da ya zo sai muka yanke shawara kan da a tafi asibitin koyarwa, gara a kai shi kyamis na Karkari.
“Da ta tafi asibitin Karkari da wannan yaron, bayan ta tafi da kamar mintuna uku zuwa hudu haka, sai kuma ga yar wannan yaron ita ma ta kamu ba ta da lafiya, sai ta kama kafafuwanta da hannayenta suka kama mimmikewa. Mata suka zo suka kama yi mata addu’o’i sannan ni ma na zo na yi mata addu’o’i, karshe dai ita ma cikin minti biyu aka dauke ta aka kai ta waccan kyamis din da aka tafi da kaninta.
“Duka ba a fi minti biyar ba sai kuma yayarta ita ma aka ce ba ta da lafiya, ita ma ni na dauke ta a babur da wanta muka sake zuwa wancan kyamis. Wannan likita ya dudduba ta sai ya ba da shawara a dauke ta a kai ta babban asibiti na Gwarzo, sun tafi babban asibiti sai ita kuma wannan mara lafyar ta biyu kamar cikin mintuna kalilan sai ta rasu, aka dauko ta aka taho da ita gida.
“Shi kuma karamin, da ya fara kamuwa aka taho gida domin a samu ‘yan kudi a tafi wani asibitin, tun da shi wannan mai kyamis ya nuna dai a je gaba. Waccan yarinya da aka tafi Gwarzo da ita an yi nisa an tasamma Gwarzo sai rai ya yi halinsa. To aka dawo gida, wacce ta fara rasuwa an yi jana’izarta, mutane wasu sun tafi wasu kuma suna nan ana ta juyayi, sai aka ce ita ma ga ta an kawo ta, ta rasu!”
Adamu ya ci gaba cewa, “Muna nan a zaune, shi wannan dan karamin na farko, an dauko shi za a tafi wani asibitin duk dai a kofar gidan da aka yi rasuwar shi ma sai ya rasu, kin ga guda daya an yi jana’iza biyu kuma ga su za a yi tasu. Bayan yamma ta yi, sai babbansu dan marigayiyar kenan, wajen magariba, shi ma sai ya ce cikinsa yana dan juya masa, wani a cikin gidanmu matashi sai ya ce to ya je kyamis ya karbi magani, daga nan dai shi ma aka dauke shi zuwa babban asibitin Gwarzo, shi ma likita ya dudduba shi aka rubuta magani aka ba shi ya sha aka dawo da shi gida.”
“Da daddare mun fara bacci, a cikin dai iyalin sai wani shi ma ya kamu ba shi da lafiya, kuma aka sake daukar sa muka tafiya asibiti, wannan wanda aka sake daukarsa shi ne aka rubuta magunguna aka ba shi, amma shi an ga afuwa a jikisa domin a ranar Laraba (ta makon jiya) yaron yana raye, amma ranar Alhamisi da safe shi ma ya ce ga garinku nan, suka zamto masu rasuwa mutum hudu kenan.”
“A wannan rana ta Alhamis, ita wannan mahaifiya tasu ita ma ta ce ga garinku nan. Ranar Alhamis dadaddare shi wannan babban matashin muka dauke shi misalin karfe uku da mintuna na dare shi ma muka kai shi asibiti, ranar Alhamis daddadare jikin nasa ya matsa, aka ba da shawara daga likitoci cewar a tafi Kano da shi, shi ma muka tafi Kano, a ranar Juma’a (ta makon jiya) da hantsi, sai aka kira aka ce shi ma Allah ya karbi abinsa. Wannan shi ne dan takaitattcen abin da zan gaya muku.”
To ko ta yaya aka gano abin da ya yi sanadin mutuwarsu? Malam Yahaya ya ce, “A kan rasuwarsu, hasashen da aka yi da tunani, akwai babban dan marigayiyar nan da kansa kafin larura ta same shi ya ce, anya abin da mahaifiyarmu ta yi mana abinci da shi ina tunaninsa (shi ne matsalar), kwanan baya ta taba dauko wata dusa ta koko wai za ta yi musu abinci, shi da kansa ya hana ta ya ce ka da ta yi domin ya ga kamar (dusar) ta tsufa a bar ta, to kaddara.
“Akwai dan mijinta wanda shi gidan a hannunsa yake, yana kokari, duk ranar da Allah ya buda ya samo da yawa kowa a gida zai wadata bangaren abinci, ranar da ya samo kadan, kowa sai dai ya dan taba ya yi hakuri, ranar da kuma Allah bai bayar ba, to kowa kuma sai dai ya rike kansa. To sai aka zo kan wannan gabar da kowa zai rike kansa, to sai yake tunanin wancan abinci da mahaifiyar ta yi suka ci a nan larurar take. A hasashe duk muka yi, wancan abu (dusa) da aka dauko shi ni na duba, dusa ce ta koko sannan akwai yana a ciki, akwai gashin kaji a ciki, za ka iya samun kashin bera ma, to a hasashe (muka ce) shi ne (matsalar) gaskiya.”
Da wakiliyarmu ta tambaye shi cewa, an ce likitoci sun zo sun dudduba ko sun ga dusar kuma an auna ta? Malam Yahaya ya ce, “Gaskiya dusar babu likitan da ya ganta, dalili kuwa da aka gano (bisa hasashe) ita ce, ni na karbe ta, tun da muna kauye ina kiwon kaji da zabi da tumaki haka, an yi shawara a juye ta kan juji, sai na ce gaskiya a’a, ba mu so a sake rasa ran ko dan tsako ne, hakan asara ce, sai na karbe ta gaba daya, ni ne nan na kone ta, kuma ni ina matsayin kanin mahaifin wadanna mamata ne, da mahaifinsu da ni uwarmu daya ubanmu daya. Don haka na ga bari na yi anfami da wannan dama na kone ta domin hankalinmu ya kwanta.”
Adamu ya ci gaba da bayani a kan yadda sauran mutanen gida suka ci abincin, amma abin bai yi tasiri ba sosai a kansu ha rya kai ga mutuwa.
“Ai ko wannan abincin da ta yi suka ci da ‘ya’yanta, bisa ga al ’adarmu ta mutanen kauye idan aka yi abinci ana irin kawo kwaryar nan a rika rabawa wuri-wuri, to ita a hashena, ‘ya’yanta sun ci abincin da yawa ne, amma akwai yara, misali an kai wannan daki, wata ‘ya’ya biyar ne da ita za a ba ta kamar guda biyar ko shida, to kowa zai dauki dai-dai, saboda haka kin ga ba za ki hada da wadanda suka ci suka koshi ba, domin wadancan (da suka ci a cikin mutanen gidan) ba su ci da yawa kamar su ba,” in ji shi.
Tsokacin kishiyar marigayiyar, Ramma Abdulkadir
Wakiliyarmu ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen jin ta bakin kishiyar marigayiyar wadda ita ma wasu daga cikin ‘ya’yanta sun ci Gaudar amma rashin lafiyarsu ba ta yi tsanani ba har Allah ya sa suka murmure, Ramma Abdulkarim, inda ta yi nata bayanin kamar haka:
“Ni dai abin da ya faru, marigayiyar ta ce an yi haihuwa a garinsu za ta gidansu, da ta dawo sai ta ce Gauda za ta yi, ta zo da dusar kokonta, ta daka ta dora wa danta ya dawo aka hada wannan Gauda suka zuzzuba abinsu suka ci, mu kuma ta zuzzuba mana ina da ‘ya’yana tara, su biyar na ba su wannan gauda bibiyu, dan karamin dana ya sa kuka ya ce zai kara, na ce hakuri za ka yi, yanayi ne (na yunwa) Allah ya riga ya kawo mu, abin da kowa ya ci hakuri yake wa ransa, in mun ci mu hakura, in ma ba mu ci ba hakuri za mu yi, wannan shi ne abin da ya faru,” in ji Ramma.
Bugu da kari, Ramma ta musanta kalaman da ake ake yadawa na cewa, ‘yan mata biyu na marigayiyar da suka rasu an sa ranar bikinsu. “Ba haka ba ne, tana da yara mata guda biyu da suka fara tasawa, sai kuma uku su kenan.” Kamar yadda ta bayyana.
Sai dai kuma, bincikenmu ya gano cewa, asali ba dusar kokon da suka yi amfani da ita ta yi ajalinsu ba, ruwan da aka yi amfani da shi ne wurin girka Gaudar wadda aka tabbatar wata katuwar tsaka ta dade da mutuwa a ciki.
Majiyarmu ta bayyana cewa, “Kin san ana cikin yanayin halin rayuwa, wani gidan ma sai a yi kwana da kwanaki ba a dora tukunya ba, to matar sun galabaita da yunwa ita da ‘ya’yanta, sai ta samo dusar gero wacce aka tace ta dauka ta kai aka markada, to akwai wani abu gauda-gauda ta sarrafa shi da dusar suka ci ita da ‘ya’yan nata, sannan ta zuba wa kishiyarta wato abokiyar zamanta ita ma ta ci.
“A lokacin da suka ci, babu abin da ya yi musu sai zuwa wasu ‘yan awanni sai yaran suka fara rashin lafiya, aka dauke su aka kai su asibiti, wasu daga cikin yaran ma kafin a kai su asibiti sun rasu, sauran kuma bayan da aka kai su asibiti ana cikin ba su taimkaon gaggawa suka rasu…
“Likitoci na ta bincike domin gano musabbabin mutuwarsu, domin cin dusa kadai ba zai yi sanadiyyar mutuwarsu ba tun da dusa babu guba a cikinta, kuma ko da dabbobi ne suka ci a wani lokacin ma sai dai su yi gudawa.
“To da likitoci suka zurfafa bincike sai suka gano ashe tsaka ce sanadiyyar mutuwarsu, yadda lamarin ya kasance shi ne, wadannan bayin Allah suna rayuwa ne a wani kauye da ake kira da Karkari, kuma gari ne da suke fama da karancin ruwan sha, ta yadda za ka ga kowane gida akwai jaraku na diban ruwa domin tara ruwa.
“A lokacin da aka zo da jami’an ‘yansanda da likitoci bincike ya tsananta sai aka rika bin irin wadannan jaraku na ruwa ana dubawa ko za a samu wata alama, aka rika zubar da ruwan da ke cikin jarakun, sai da aka zo kan wata jarka sai aka samu wata tsaka a ciki ta mutu har ta kumbura suntum! Kuma wannan jarkar ita ce jarkar da wannan mata ta yi amfani da ruwan ciki wanda shi ne sanadiyyar rasuwarta da ‘ya’yanta.” In ji majiyar tamu.
…Mutane 18 Suka Rasu Sakamakon Cin Gishirin Kunshi Da Maganin Kwari A Sakkwato Da Zamfara
Akalla mutane 12 ne suka mutu a garin Daki Takwas da ke karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara, bayan shan miyar ganyen lalo mai dauke da maganin kashe kwari.
Mutane 25 ne da suka fito daga gidaje biyu suka sha miyar a ranar Juma’ar makon jiya, inda tun a lokacin suka fara rasuwa.
Zuwa lokacin rubuta wannan labari, akwai mutane tara daga cikinsu da ke kwance a asibiti.
Daraktan Kula da Lafiyar Al’umma kuma jami’i mai Kula da cututtuka masu yaduwa a jihar, Dakta Yusuf Abubakar Haske, ya bayyana yadda al’amarin ya faru, inda ya tabbatar da cewa shan miyar da aka yi da ganyen lalon ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.
“Manomi ne ya je ya yi feshin kwari a kan abin da ba ya so, daga ciki akwai wani ganye da ake kira lalo, wanda ana miya da shi a gidajenmu na Hausawa. Su kuma mutanen ba su san ya yi ba.
“Ya yi feshin da safe, su kuma suka je da rana domin nemo ganyen da za su yi miya. Daga bisani sai suka kamu da amai da gudawa da zubar da yawu. Daga nan ne aka dauke su zuwa asibiti, domin a ba su taimakon gaggawa.”
Ya kara da cewa, kasancewar wasu sun fi wasu shan miyar, sai ya kasance wasu sun mutu a gida yayin da wasu kuma a wani asibiti a Anka suka mutu. Wasu kuma sai da aka kai su Babban Asibitin Tarayyar jihar sannan suka rasu. Amma ya ce jihar ta shirya don tunkarar lamarin.
Mutum 6 ‘Yan Gida Daya Sun Rasu Bayan Cin Gishirin Kunshi A Abinci A Sakkwato
A wani labarin kuma, kimanin mutane shida iyalin wani mutum mai suna Ummaru Ladan ne suka rasu, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara 10, bayan sun yi kuskure wajen amfani da gishirin kunshi a girki maimakon gishirin abinci.
Lamarin ya faru a garin Kaura da ke karamar hukumar Shagari, a Jihar Sakkwato.
Iyalan sun dafa miya ne da “Gishirin kunshi” (gishirin da ake amfani da shi wajen hada lalle) a ranar Laraba (ta makon jiya). Kana sun sake dumama abincin da safiyar ranar Alhamis kafin su ci.
A cewar Kabiru Muhammad, wani dan uwan mamatan, karamar yarinyar ce ta fara rasuwa bayan ta fara jikata a ranar Alhamis, bayan an yi mata maganin zazzabin cizon sauro.
Muhammad ya ce, “A ranar Alhamis kowa a kauyen ya ga yarinyar tana yawo. Ta rasu ne a safiyar ranar Juma’ar da ta gabata. Bayan ta rasu ne, sauran mutanen gidan suka fara rashin lafiya, don haka muka dauke su zuwa Babban Asibitin Shagari.
“Bayan mun isa asibitin ne, matar Alhaji Ummaru ta rasu. Don haka muka hade sallar jana’izarta da ta yarinyar. Likitocin asibitin sun tabbatar lamarin ya fi karfinsu, don haka suka ce mu kai su Babban Asibitin Jihar Sakkwato, UDUTH.”
“Amma kafin su yi wannan jinyar, wani mutum ya rasu a ranar Asabar, don haka muka dauki marasa lafiya uku zuwa Sakkwato”
Ya kara da cewa, “A UDUTH, biyu daga cikinsu suka sake rasuwa, kuma a ranar Litinin wani ya sake rasuwa, don haka muka yi jana’izarsa.
“Mutanen da suka rasu sun hada da daya daga cikin matan Alhaji, da dansa, da matan ‘ya’yansa biyu, da kuma jikokinsa biyu,” in ji shi.
BBC Pidgin ta ruwaito cewar da aka tambaye shi ta yadda suka gano gishirin kunshi ne ya yi sanadin mutuwarsu, Muhammad ya ce wata yarinya daga cikin ‘yan gidan ce ta gano an yi kuskuren amfani da gishirin a ranar Juma’a, yayin da suke neman gishirin da za su yi amfani da shi.
Sun gano cewa ba su yi amfani da gishirin da ya dace a abincin ba, wanda hakan ya sa suka fara bincike har suka gano gishirin kunshi ne aka zuba a abincin.
Dan Modi Sahabi, wanda dan uwa ne ga Alhaji Ummaru, ya ce magidancin ya ci abincin amma kadan ba da yawa ba, shi ya sa aka sallame shi daga asibiti bayan ya samu kulawar likitoci.
Sahabi ya ce, “Yanzu haka, Alhaji Ummaru yana cikin matsanancin firgici, kuma ba zai iya magana da mutane ba saboda halin da yake ciki yanzu.”
Mutanen garin sun bayyana wadanda suka rasun a matsayin mutane masu son juna, zaman lafiya, kuma masu zumunci da kowa a garin.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar Sakkwato, Hajiya Asabe Balarabe, ta ce ba a tuntube su ba lokacin da lamarin ya faru, wanda ta ce da sun samu labarin faruwar lamarin a kan lokaci da sun yi kokarin ba su agajin gaggawa.
Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan wasu mutane shida sun mutu sakamakon guba a abinci a Jihar Sakkwato.
Baya ga jihohin Kano da Sakkwato da Zamfara, har ila yau, wasu rahotanni sun nunar da cewa akwai karin mutane da suka rasu a ‘yan makonnin nan sanadin cin abinci mai guba a Jihohin Kogi da Nasarawa da Kwara da kuma Anambara, ciki har da wata tsohuwa mai shekaru 70 a duniya tare da danta mai shekara 34 a Ilorin.