Bai kai makonni 2 ba da sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta fara aiki, amma ta riga ta kaddamar da matakin hukuncin harajin kwastam kan kasashe daban daban, lamarin da ya janyo suka da damuwa daga jama’ar kasashen duniya. Sakamakon wani binciken ra’ayin al’ummun duniya da kafar watsa labarai ta CGTN ta kasar Sin ta yi, ya nuna cewa, dimbin mutanen da suka amsa tambayoyin binciken sun bayyana matakin karbar karin harajin kwastam da kasar Amurka ta yi a matsayin wanda zai illata tattalin arzikin duniya.
Ban da haka, sakamakon binciken CGTN ya nuna cewa, kaso 90.53% na mutanen da suka amsa tambayoyin da aka yi musu, sun ce yadda gwamnatin kasar Amurka ta dauki jerin matakan kariyar cinikayya ya kasance keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, yayin da kaso 90.68% na mutanen sun ce matakan kasar Amurka na matsawa sauran kasashe lamba sun nuna yadda kasar ke nuna fin karfi da babakere a duniya. Haka zalika, kaso 92.14% na mutanen da aka yi musu tambayoyi sun ce matakan matsin lamba na kasar Amurka sun haifar da babbar illa mai dorewa ga tattalin arzikin duniya.
CGTN ta samu wadannan alkaluma ne bisa binciken jin ra’ayin jama’a da ta gudanar kan mutane 14071 a kasashe 38, wadanda suka hada da kasashe masu sukuni irinsu Amurka da Birtaniya da Canada, gami da kasashe masu tasowa kamarsu India, da Afirka ta Kudu, da Brazil, da dai sauransu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp