Matsalar sauyin yanayi ta ci gaba da shafar duk fadin duniya a halin yanzu, inda ake kara bukatar karfin gwiwa da daukar matakai na zahiri don tinkarar matsalar. Kafar watsa labarai ta CGTN dake karkashin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ya hada kai tare da jami’ar Renmin ta kasar Sin, don gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma dake kunshe da mutane 7658 daga kasashe 38, inda kaso 90.3 bisa dari na masu ba da amsa a binciken ke ganin cewa, akwai bukatar shawo kan matsalar sauyin yanayi ba tare da bata lokaci ba, kana ya zama dole sassan kasa da kasa su cimma matsaya tare da kara daukar matakai na zahiri.
Yarjejeniyar tinkarar matsalar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, a tarihi da kuma a halin yanzu, kasashen da suka fi fitar da hayaki mai gurbata muhalli, kasashe ne masu hannu da shuni, don haka an tsara wata manufa dake cewa, kasashe masu arziki da kasashe masu tasowa, ya kamata su dauki nauyin shawo kan matsalar sauyin yanayi tare, amma akwai bambancin nauyin dake wuyan kowa. Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa, kaso 75.3 bisa dari na masu ba da amsa na ganin cewa, kasashe masu arziki ba su nuna sahihiyar aniya ko daukar matakai na zahiri a fannin tinkarar sauyin yanayi dake addabar duniya ba, al’amarin da ya raunata hadin-gwiwar kasa da kasa wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi. Sai kuma kaso 73.9 bisa dari dake ganin cewa, kasa cika alkawarin tallafa wa ayyukan tinkarar matsalar sauyin yanayi da kasashe masu hannu da shuni suka yi, abu ne dake nuna kin sauke nauyin da ya rataya da su. Sa’annan kaso 85.8 bisa dari na masu ba da amsar sun bukaci kasashe masu arziki, da su samar da tallafin kudi mai tsoka ga kasashe masu tasowa, don aiwatar da yarjejeniyar Paris a zahirance.
Daga cikin masu ba da amsa a binciken, akwai wadanda suka fito daga kasashe masu arziki, ciki har da Amurka, da Jamus, da Japan, akwai kuma wadanda suka fito daga kasashe masu tasowa, ciki har da Argentina, da Indiya, da kuma Kenya. (Murtala Zhang)