Wani rahoto mai ban mamaki daga kwamitin kula da harkokin jama’a na majalisar dattawa ya nuna cewa, bindigogi 3,907 yawancinsu kirar AK-47 sun ɓace daga hannun rundunar ‘yansanda a fadin Nijeriya.
An gano hakan ne bayan da ofishin babban mai tattara bayanai na tarayya ya kakkaɓe daftarin rundunar ‘yansandan Nijeriya.
- Waɗanda Suka Sace Jigo A Jam’iyyar APC Sun Buƙaci A Biya Su Naira Miliyan 350
- Babu Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Tsarinmu – Gwamnan Zamfara
Rundunar ‘yansandan Nijeriya tana da sashen bincike da tsare-tsare, wanda ke da alhakin gudanar da bincike akai-akai na sassan ‘yansanda, don tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace.
A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.