Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, bisa yadda aka tsara yanayin Birnin Tarayyar Abuja da kuma yadda birnin ya kasance, yana da albarkatun noma, hakan zai bai wa Hukumar NPA damar ci gaba da wata karfafa kokarin Gwamnatin Tarayya na, bunkasa samar da kudaden shiga, daga fannin da bai bai shafi harkar Man Fetur ba.
Dantsoho a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a da ta gabata, taron baje koli na kasa da kasa da cibiyar kasuwanci ta Abuja ta shirya ya ce, kasancewar birnin a tsakiyar kasar nan, hakan zai kuma taimaka wa Hukumarsa, cimma kudurinta na kara habaka hada-hadar kasuwanci.
- An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi
- Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
“Kasancewar yanayin na Abuja za ta samar da damar amfana a bangaren hada-hadar fitar da kaya daga cikin kasar nan, zuwa ketare”Inji Dantsoho.
Shugaban ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancinsa, Hukumar za ta yi namijin kokari wajen bayar da goyon bayanta, wajen fitar da kayan da ba su shafi dangogin Mai ba, zuwa kasar waje, musamman ta hanyar cin giyar albakatun yanayin na Abuja da kuma na bangaren aikin noma, da birnin ke da shi. Ya kara da cewa, ta hanyar wadannan alkatun kasar da birnin ke da su, Hukumar za ta kara bayar da gudunmwarta, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan da kuma kara fitar da kayan da ba su shafi Man ba, zuwa ketare.
A cewarsa, domin Hukumar ta tabbatar da na kara mayar da hankalin wajen ganin ana bin ka’ida da kuma tabbatar da ingancin gudanar da ayyukanta, ta kirkiro da tsare-tsare na fasahar zamani na bai daya da ake kira a turance, PCS da kuma NSW.
A cewarsa, wadannan fasahar ta zamani, za su taimaka wajen hada masu ruwa da tsaki a fannin da ke fitar da kaya zuwa ketare tare da kuma rage jinkiri wajen fitar da kayan waje da kuma samar da kyakyawan yanayi ga masu fitar da kayan ketare.Shugaban ya sanar da cewa, Hukumar na alfaharin danganta manta da ayyukan da Cibiyar ta kolin kasuwanci ta Abuja ke ci gaba da gudanarwa musamman a bangaren kara habaka tattalin arzikin kasar nan.
Dantsoho ya kuma gayyaci masu ruwa da tsaki a fannin kar su bari a barsu a baya, wajen cin gajiyar saukin da Hukumar ta samar na fitar da kaya daga cikin kasar nan, zuwa ketare.
Kazalika, Shugaban ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma samar da tsarin fasahar zamani na fitar da kaya a cikin sauki a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar wato EPT.
Ya kara da cewa, wannan fasahar ta taimaka matuka wajen fitar da kaya waje ba tare da wani tarnaki ba.
Shugaban ya ci gaba da cewa, Hukumar ta kuma fadada fasahar ta EPT, domin samar da saukin fitar da kaya ga kananan da matsakaitan masana’antun kasar suka sarrafa, domin fitar da su ketare.
Hakazalika, Shugaban ya bayyana cewa, domin ayyukan Hukumar su tafi kafada da kafada da kudurin Gwamnatin Tarayya NPA ta saita gudanar da ayyukanta ta hanyar yin amfani da fasahar ta zamani ta PCS.
A cewarsa, wannan zai tabbatar da samar da wani ginshike ga fasahar NSW, inda za a rinka fitar da kayan waje, ba tare da wata matsala ba.
Dantsoho ya yi nuni da cewa, fasahar ta NSW aba ce, da ake yin amfani da da ita, a daukacin fadin duniya, wajen samar da saukin fitar da kaya waje.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, Hukumar na daukar Malamai wajen ganin cewa, ayyukanta, sun kai da lungu da sako, da ke da wuyar isa a kasar.
Ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yau, kofar Hukumar a bude take domin yin hadaka da su.