An ɗaure wasu ‘yan Nijeriya 4 a kasar Birtaniya bisa samun su da laifin buga jabun takardar aure 2,000.
Abraham Alade Olarotimi Onifade, Abayomi Aderinsoye Shodipo, Nosimot Mojisola Gbadamosi da Adekunle Kabir, an yanke musu hukuncin daurin shekaru13 bayan sauraron karar da aka yi a kotun Woolwich Crown da ke Landan, ranar Talata.
- Tinubu Zai Kai Ziyara Kasar Sin Domin Haɓaka Tattalin Arziki Da Kayayyakin More Rayuwa
- Kotu Ta Ɗaure Hadimin Tambuwal Kan Yaɗa Bidiyon Da Ake Yi Wa Matar Gwamnan Sakkwato Liƙi Da Dala
Tsakanin Maris 2019 da Mayun 2023, an ce waɗanda ake tuhuma sun haɗa baki domin kwarewa kan sanin dokokin tsuguno a tsarin kasashen tarayyar Tutai (EU).
Sun buga jabun takaddun shaidar aure na al’ada na Nijeriya da sauran takaddun zamba don tallafawa wasu ‘yan Nijeriya don ci gaba da zama a kasar Birtaniya.
Fiye da takardun auren bogi 2,000 da mutanen suka yi, an gano su ne ta hanyar wani bincike da aka yi tare da hadin gwiwar ‘Home Office International Operations’ da ke Legas.