Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya zayyana wasu matakai da za a bi domin tsaurara dokokin shiga da zama a kasar, da zimmar rage kwarorowar baki masu zuwa zama da karatu da neman aiki.
Daga cikin matakan akwai gwajin Ingilishi ga dukkan masu neman izini shiga kasar da kuma tsawaita lokacin da ake dauka a kasar kafin samun izinin zama na dindindin.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Sin Da Birtaniya Da Su Kiyaye Tsarin Kasa Da Kasa Da Aka Kafa Bayan Yakin Duniya Na Biyu
- An Kama Miyagun Kwayoyi Kan Hanyar Zuwa Birtaniya A Filin Jiragen Saman Legas
Firaministan yana kuma so a rage daukar ma’aikatan jinya daga kasashen ketare, matakin da zai taimaaka wajen rage yawan ‘yan ksashen waje da ake dauka aiki a kasar ta sahihiyar hanya.
Sai dai bai ce komai ba game da masu shiga kasar ta barauniyar hanya, kamar masu shiga ta teku.
Adadin bakin da suka shiga kasar a shekarar 2024 sun kai 728,000 zuwa watan Yunin shekarar.
Hukumomin kasar za su fitar da gamsasshen bayani mai dauke da sababbin tsauraran matakan, wadanda za su kunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya.
Sakataren harkokin baki na Birtaniya Ybette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage daukar ma’aikatan jinya daga kasashen waje.
Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage kusan mutum 50,000 wadanda ba kwararru ba ne sosai da suke shiga kasar daga kasashen ketare a duk shekara.
Firaministan ya ce sababbin matakan za su taimaka wajen “sake mallake bakin iyakokin kasarmu.”
Idan aka dabbaka sabbin matakan nan da gwamnatin kasar za ta dauka, ‘yan kasashen mutane daga kasashen Nijeriya da Pakistan da Sri Lanka za su fuskanci kalubale wajen samun izinin shiga kasar Birtaniya domin karatu.
Abin da hakan ke nufi
Starmer ya ce Birtaniya za ta rika neman wadanda suka fi kwarewa ne a duniya wajen daukar aiki, sannan za su bincika me ya sa wani bangaren aikin kasar ya fi mayar da hanakali kan “neman sauki wajen daukar aiki.”
Firaministan ya ce sabbin matakan za su fayyace komai da komai game da tsare-tsaren shige da fice a kasar – iyali da karatu da aiki.
“Zan tabbatar da matakan nan saboda za su tabbatar da adalci, kuma abin da ya dace ke nan,” in ji Starmer a wani taron manema labarai.
Ya ce bai kamata a rika mayar da hankali kan neman sauki wajen daukar ma’aikata ba, maimakon mayar da hankali kan horar da matasan kasar.
Starmer ya kara da cewa bakin da suke shigowa kasar a gwamnatin baya sun kai kusan miliyan 1 a shekarar 2023, wanda shi ne adadi mafi yawa.
Ya ce adadin bakin ya kai adadin mutanen birnin Birmingham baki daya, wanda kuma shi ne birni na biyu mafi girma a Birtaniya.
“Wannan ba ci gaba ba ne, kasada ce. Ba zai yiwu a ce da kuskure hakan ya faru ba, wannan ganganci aka yi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp