Kamfanin dillanci labarai na Bloomberg ya ruwaito a jiya Laraba cewa, kasashen Amurka da Turai suna damuwar cewa, karfin da kasar Sin ke da shi wajen samar da motoci masu amfani da wutar lantarki wato EVs da na’urorin samar da makamashi bisa hasken rana na iya shafe masana’antun ketare, damuwarsu ba ta da tushe.
Rahoton ya ce, idan aka ambato batun EVs, to, matsalar da kasashe masu ci gaban tattalin arziki suke fuskanta ita ce, kamfanonin kera motoci na kasar Sin sun fi samar da karin motoci ba tare da kashe kudi da yawa ba da kuma yin tasiri a kasuwanni, saboda fasaharsu, da tsarin samar da kayayyaki na gida, da sabbin ababen more rayuwa ta fuskar sufuri, da amfani da makamashi da kasa masu rahusa.
“Daga mahangar sauran kasashen duniya, idan ana samar da kayayyaki fiye da yadda ake bukata, to, farashin kayayyakin zai ragu. Yawan motocin da kasar Sin ta sayar zuwa ketare ya karu sosai a bara, kasar ta zarce Japan a matsayin kasar da ta fi fitar da motoci a duniya, kuma hakika farashin motocin kasar Sin ya karu. Hakan na nufin karuwar bukatarsu ba saboda raguwar farashinsu ba.” a cewar rahoton.
Game da na’urorin samar da makamashi bisa hasken rana kuwa, rahoton ya ce, akwai yuwuwar yawan bukatu a nan gaba zai iya zarce yadda ake tsammani. Wannan kiyasin yana da muhimmanci, musamman ga kayayyaki marasa gurbata muhalli, saboda kila za a daga matsayin rage fitar da hayakin carbon mai dumama yanayi a cikin shekaru masu zuwa. (Yahaya)