Kwannan nan, bisa alkaluman tattalin arzikin Sin na rubu’in farkon shekarar bana da aka fitar, hukumomin hada hadar kudade na kasashen ketare kamar Bankin Deutsche, da Goldman Sachs, da kuma UBS, sun kara daga hasashensu na karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar bana. A daya bangaren, yayin da hukumomin suka bayyana imanin su ga tattalin arzikin Sin, sun kuma bayyana kwarin gwiwarsu game da damammakin zuba jari cikin sassan hada-hadar kudin kasar Sin.
Game da yanayin tattalin arzikin Sin a shekaru 5 masu zuwa kuwa, kafar watsa labarai ta Bloomberg dake Amurka, ta yi hasashen cewa, Sin za ta zama kasa da ta fi ba da gudummawa ga karuwar tattalin arzikin kasa da kasa nan zuwa shekaru 5, kuma kason gudummawarta zai wuce jimilar kason gudummawar dukkanin kasashen kungiyar G7, wanda zai rubanya na kasar Amurka da kusan ninki 2. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp