Gaggauta Buɗa-baki yana tabbatar da mutane a kan sunna. Akwai hadisai a kan haka:
1. An karɓo hadisi daga Sahlu dan Sa’adu Allah Ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Al’ummata ba za ta gushe a kan sunnata ba, matuƙar ba ta jirkinta buɗa-bakinta zuwa fitowar taurari ba “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan yana azumi sai ya umarci wani mutum ya hau wani abu mai tudu ya ga rana ta faɗi, idan ta fadi sai ya yi buɗa-baki. Hadisi ne ingantacce Ibnu Khumaima ne yabruwaito [#2061] da Ibnu Hibbãn [#3510] da Hãkim [#1584].
2. An karɓo hadisi daga Anas dan Malik Allah Ya ƙara yarda a gare shi ya ce: “Ban taɓa ganin Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya yi sallar magriba ba (alhali yana azumi) face sai ya yi buɗa-baki ko da kuwa da maƙwalwar ruwa ne “Hadisi ne ingantacce Ibnu Hibbãn [#3504] da Abu Ya’alã [#3792] da Ibnu Khuzaima [#2063] da Bazzãr [#7127].
Jinkirta ta buɗa-baki saɓa wa sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ne, kuma mutane ba za su gushe ba cikin alheri matuƙar suka aikata sunna. Duba Ibnu Dakikil Id; Ihkãmul Ahkãm [shafi na 419].
Kuma jirkinta buɗa-baki koyi ne da ahlulkitãbi, watau Yahudu da Nasara kamar yadda ya gabata a hadisi. A cikin Musulumi an samu waɗanda suke kwaikwayon Yahudu da Nasara wajen jinkirta buɗa-baki, ba sa gaggauta yinsa, waɗannan mutane su ne ‘yan Shi’a, kuma suna ƙudurce jinkirta shi, shi ne daidai. Waɗannan hadisai da aka ambata suna yi musu martani.
Jinkirta buɗa-baki alama ce ta ‘yan bidi’a. Duba as-San’ani; Subus Salam [2/221].
Imam as-Shãfi’i Allah ya yi masa rahama yana cewa: “Ina son gaggauta buɗa-baki, da ƙin jirkinta shi, kuma ina ƙyamar hakan ne ga wanda ya jinkirta shi da gangan kuma yake ganin haka shi ne abin da ya fi falala” Duba as-Shãfi’i; al-Ummu [2/106].