Wata budurwa ‘yar shekara 20 mai suna Fatima Aliyu, a ranar Litinin ta roki kotun shari’a da ke Kaduna a jihar Kaduna da ta hana mahaifinta, Aliyu Muhammad aurar da ita akan dole.
Fatima, wacce ta yi magana ta bakin lauyanta, Malam Y. A. Bulama, ta shaida wa kotun cewa tana da wanda take so.
Bulama ya ce, “Mahaifin wacce ya ke karewa da ta ke zaune a gidan goggonta, yana son aurar da ita ga wani mutum a kauyensu kuma ya yi barazanar tafiya da ita zuwa kauyen don yi mata auren dole a kauyen da ke jihar Neja.
Bulama ya bayyana cewa, wacce ya ke karewa, ba ta kai mahaifinta kara kotu ba ne don rashin girmama shi.
A nasa bangaren, mahaifin ya ce iyayensa da suka rasu ne suka zabar wa ‘yarsa ango tun suna raye kuma dole ya mutunta burinsu.
Ya ce, “Na aurar da ’ya’yana mata shida a kauyen kuma suna nan lafiya. Mahaifiyar Fatima ita ce ke zuga Fatima kan kin amince wa da bukatar aurar da ita.
Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman, ya ce Mahaifi na da hakkin ya zabar wa ‘yarsa mijin aure a karkashin hukuncin kotun shari’ar.
Sai dai ya ce ba a son auren dole, don haka ya shawarci mahaifin yarinyar da ya kara yin hakuri da ‘yarsa.
Alkalin ya kara da cewa, “Kai ne mahaifinta. Don haka, ya kamata ka yi mata addu’ar samun miji mafi da cewa, domin idan kana fushi da ita ba za ta ga abubuwa masu kyau ba a rayuwarta.
“Ka ba ta damar gabatar da wanda take son aura, sai ka duba addininsa da halayensa, idan sun da ce, ka amince mata auran shi.”
Ya kuma shawarci Fatima da ta zama diya mai mutunci da tarbiyya (NAN).