Wata budurwa da rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, ta bayyana sunanta da Florence Vandi, wacce ma’aikaciyar jinyace a Girei, ta kashe kanta, sa’o’i kaɗan bayan mutuwar saurayinta.
Marigayiya Florence Vandi, da ke zama a unguwar Viniklang a karamar hukumar Girei, ta kawo karshen rayuwarta ne biyo bayan Shan Fiya-fiyar da ta yi.
- Fintiri Ya Gabatar Da Kasafin 2024 A Gaban Majalisar Dokokin Adamawa
- Jami’in MDD: Kasar Sin Ta Ba Da Babbar Gudummawa Ga Wadatar Abinci A Duniya
Cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar, ta ce “Vandi mai shekaru 22, ta kashe kanta ne a ranar 12/12/2023, ta hanyar shan maganin kwari (Fiya-fiya).
“Vandi ta dauki mummunan matakin ne, ‘yan sa’o’i kadan da mutuwar saurayinta da ake kira Nuhu Boniface, da ya rasu bayan aikin da aka yi mishi a asibiti.
“Bincike bayan mutuwarta ya tabbatar da cewa, Florence ma’aikaciyar jinyace, da take aiki da hukumar bada lafiya matakin farko (Girei Primary Health Care Centre)” inji sanarwar.
Ta kara da cewa shugaban rundunar ‘yansandan jihar, CP Afolabi Babatola, da ya bayyana lamarin da cewa abin takaici da bakin ciki, ya shawarci jama’a da su daina daukar doka a hannu.