Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari a matsayin ɗan kishin ƙasa, soja kuma dattijo, wanda ya hidimtawa ƙasa cikin girma da daraja da kuma gaskiya da riƙon amana da sadaukarwa.
A wata sanarwa da shugaban ƙasar ya sanyawa hannu da kansa, Tunubu ya sanar da rasuwar tsohon shugaban a wani asibiti a birnin Landan a yau Lahadi 12, Yuli 2025.
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari
“Na kaɗu sosai da samun labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, wanda na gada, wanda ya koma ga mahaliccinsa a yau” cewar shugaba Tinubu
Shugaban ya bayyana rayuwar Buhari a matsayin babban rashin wanda ya yi wa ƙasa hidima, daraja da kuma sadaukar da kai wajen haɗin kan ƙasa da ci gabanta.
Shugaba Tinubu ya ce Buhari ya mulki Nijeriya a lokaci mai tsauri, na farko a lokacin mulkin soja da kuma farar hula, kuma ya yi mulkin bisa adalci da ƙwarin guiwa da kuma gaskiya tare da yaƙinin cewa Nijeriya za ta samu ci gaba.
Tinubu ya ce sun yi magana da matar marigayin, Hajiya Aisha Buhari kuma ya yi mata ta’aziyya, sannan ya yi wa gaba ɗaya danginsa ta’aziyyar rasuwar Buhari da ƴan Nijeriya baki ɗaya.
Shugaban ƙasar ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina da al’ummar jihar, musamman masarautar Daura, inda Buhari ya taso.
Tuni dai shugaban ya bayar da umarnin sakko da tutar Nijeriya ƙasa-ƙasa na tsawon kwanaki bakwai daga yau, duka a cikin jimamin rasuwar Buharin.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya kuma bayar da sanarwar taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa ranar Talata domin domin girmama marigayi Buhari.
Tinubu ya bayar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya za ta karrama Buhari da lambar yabo domin girmama irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa.
Marigayi Muhammad Buhari dai ya rasu yana da shekara 82 a duniya, bayan ya sha jinya a birnin Landan na ƙasar Ingila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp