• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buhari Ɗan Kishin Ƙasa Ne — Tinubu

byAbba Ibrahim Wada and Muhammad
3 months ago
Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana marigayi tsohon shugaban ƙasa,  Muhammad Buhari a matsayin ɗan kishin ƙasa, soja kuma dattijo, wanda ya hidimtawa ƙasa cikin girma da daraja da kuma gaskiya da riƙon amana da sadaukarwa.

A wata sanarwa da shugaban ƙasar ya sanyawa hannu da kansa, Tunubu ya sanar da rasuwar tsohon shugaban a wani asibiti a birnin Landan a yau Lahadi 12, Yuli 2025.

  • Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari

“Na kaɗu sosai da samun labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, wanda na gada, wanda ya koma ga mahaliccinsa a yau” cewar shugaba Tinubu

Shugaban ya bayyana rayuwar Buhari a matsayin babban rashin wanda ya yi wa ƙasa hidima, daraja da kuma sadaukar da kai wajen haɗin kan ƙasa da ci gabanta.

Shugaba Tinubu ya ce Buhari ya mulki Nijeriya a lokaci mai tsauri, na farko a lokacin mulkin soja da kuma farar hula, kuma ya yi mulkin bisa adalci da ƙwarin guiwa da kuma gaskiya tare da yaƙinin cewa Nijeriya za ta samu ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Tinubu ya ce sun yi magana da matar marigayin, Hajiya Aisha Buhari kuma ya yi mata ta’aziyya,  sannan ya yi wa gaba ɗaya danginsa ta’aziyyar rasuwar Buhari da ƴan Nijeriya baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina da al’ummar jihar, musamman masarautar Daura, inda Buhari ya taso.

Tuni dai shugaban ya bayar da umarnin sakko da tutar Nijeriya ƙasa-ƙasa na tsawon kwanaki bakwai daga yau, duka a cikin jimamin rasuwar Buharin.

Shugaban ƙasa,  Bola Tinubu ya kuma bayar da sanarwar taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa ranar Talata domin domin girmama marigayi Buhari.

Tinubu ya bayar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya za ta karrama Buhari da lambar yabo domin girmama irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa.

Marigayi Muhammad Buhari dai ya rasu yana da shekara 82 a duniya, bayan ya sha jinya a birnin Landan na ƙasar Ingila.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
Next Post
Rasuwar Buhari Babbar Asara Ce Ga Nijeriya — Obasanjo

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version