• English
  • Business News
Friday, July 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya

by El-Zaharadeen Umar, Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 hours ago
in Manyan Labarai
0
Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kamar yadda kowa ya sani tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Allah ya azurta shi da masoya musamman talakawa, hakan ya kara bayyana a lokacin da aka bayyana labarin cewa Allah ya yi masa cikawa.

Abubuwan da suka biyo bayan ayyana cewa tsohon shugaban kasar fa rai ya yi halinsa, akwai sabbin abubuwan da suka bayyana sannan an kara fito da wadanda aka sani.

To, ba wannan nake son masu karatu su nutsu su karanta ba, a a wasu abubuwa ne da suka faru a ranar Talata ranar da shi marigayi ya kwanta a cikin kabarin sa na dindindin.

Kamar yadda na fada tun farko, abubuwan da suka faru suna da yawa, to amma na duba wasu guda goma da nake san jama’a su karanta ko hakan zai zama darasi a rayuwar su.

Bari mu fara da birnin Katsina kafin mu wuce Daura inda can ne aka yi jana’izar sa kuma abubuwan ban mamaki sun fi yawa a can din.

Labarai Masu Nasaba

Natasha Ta Rubuta Wa Majalisa, Tana Neman A Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu

Babu Wata Sabuwar Ƙungiyar  Ƴan Ta’adda Mai Suna Fethulla A Nijeriya – DHQ

  1. Tarihi ya nuna cewa ko lokacin da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya rasu jiragen sama da suka sauka a filin sauka da tashi na Katsina ba su kai wadanda suka sauka ba a ranar da aka yi jana’izar marigayi Muhammadu Buhari ba.

Lissafi ya nuna kusan jiragen sama tsakanin na hukumomin tsaro da na ‘yan kasuwa da wasu shugabannin daga kasashen waje kimanin jirage 33 ne suka sauka dauke da jama’a daban-daban.

Wannan ya nuna cewa jama’a sun yi tururuwa daga nesa da kusa domin halartar wannan babban taro da ya gudanar a mahaifarsa a garin Daura.

 

  1. Ban sani ko kafin dawowar dimokuradiyyar a shekarar 1999 ba, amma abin da kididdiga ta nuna shi ne, idan ba yakin neman zabe ba, babu wani lokaci da wani dalili ya hada shugaban kasa da mataimakin sa a wajen wani al’amari guda daya sai wannan rasuwar.

Babu shakka duk wanda ake ganin isashe ne a wannan kasa ta Nijeriya ya halarci jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

3. Wani abin birgewa da nuna tare da jin kai da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi shi ne yadda ya hau mota daga Katsina zuwa Daura kilomita 82 ya je ya dawo akan mota, lallai tarihi ba zai manta da wannan ba abin da ya sa wannan tafiya ta shugaba Bola ta zama wani yanki na girmama Buhari shi ne, a tsawon shekaru takwas da Buhari ya yi yana mulki sau daya ya taba zuwa Daura daga Katsina a kan mota, amma da zai dawo Katsina sai da ya hau karamin jirgi mai saukar angulu ya dawo Katsina amma Bola Tinubu ya je ya dawo a mota tsawon kilomita 164

 

  1. Ganin yadda a baya dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashe guda biyu wato Nijar da Nijeriya, inda ba a sake ganin wani abu ya hada su ba ko ta fuskar diplamasiya ba, a dalilin wannan jana’iza sai ga Firaministan Kasar Nijar Ali Lamine Zeine ya halarci wannan taro tare da tsohon shugaban kasar Nijar din Muhammadu Yusuf.

 

  1. Wani abu da kowa ne ya fahimceshi ba a lokacin wannan jana’iza shi ne, duk da irin soyayyar da ke tsakanin marigayi Muhammadu Buhari da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar sai da ya kasa yin magana da ‘yan jarida akan marigayi saboda wani irin yanayi da ya shiga na jimamanin rashin marigayi

 

  1. A safiyar ranar talata da aka yi jana’izar sa, garin Daura ya kasance tamkar kowa ya mutu duk tituna ba kowa masu sana’a sun kasa budewa tamkar lokacin ‘Corona Birus’ da aka hana al’umma fitowa.

Hakika duk wasu da suka jin zafin wannan mutuwa bayan iyalansa da ‘yan uwansa to sai mutanen Daura domin wani ya shaida mana cewa shike nan Daura ta mutu, wai shi a ganin sa hatta wutar lantarki da ake samu za su yi bankwana da ita.

 

  1. Bayan da labarin isowar gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu al’umma cewa jirgin da ya dauko gawarsa daga kasar Birtaniya ya iso Katsina, to al’umma sun yi fitar farin dango don shaida yadda jana’iza za ta kasance.

Wani abu da ya dauki hankali a daidai wannan lokaci shi ne irin yadda jama’a suka manta da cewa a wajen zaman makoki suke, lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran ‘yan adawa a Nijeriya Atiku Abubakar da shi da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf suka iso gidan Buhari, ba abinda ka ji sai kowa da maganganu na yabo da fatan alheri.

Wasu har tambaya suke yi, wai siyasa aka zo yi nan ko jana’iza, hakan dai baya rasa nasaba da cewa shi masoyinka yana tare da kai duk inda ya ganka, saboda haka ya kan manta da abinda yake a lokacin da ya ganka.

 

  1. Wato rashin ganin wasu fuskoki a wajen wannan jana’iza ya bar ayar tambaya ga mafiyawan al’umma suka je Daura musamman wadanda suka je domin su shaida wadanda suka halarci jana’izar tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Rashin ganin tsofaffin gwamnonin jihar Kano wato Abdullahi Umar Ganduje da kuma Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yasa jama’a da dama na tambayar ina wadannan mutane suka makale ne?

 

  1. Abu tara da ya ja hankali shi ne irin yadda gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya rika rusa kuka a daidai lokacin da ake kokarin yin bankwana da gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin sanya ta rami.

Wasu da dama sun bayyana wannan shiga damuwa da aka ga gwamna Dikko Radda da cewa ya tuna Allah ne domin dai kowa can zai tafi, wasu na fassara wannan kuka na shi da cewa shi kadai yasan dalilin da yasa yake rusa wannan kuka.

 

  1. Wato abu na goma a jerin abubuwan da na ce na lura da su a wajen wannan jana’iza shi ne wani abu da ba kowa ya ga shi ba, balanta ya lura da shi ya sanya shi cikin abubuwan ban mamaki da suka faru a wannan rana.

Wato lokacin da gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta iso garin Daura a Kofar gidan sa, abubuwa biyu sun faru, gwamna Malam Dikko Radda shi ne ke jagorantar ayarin Motocin tawagar shugaban kasa da kuma motar da aka dauko gawar marigayin, Dikko Radda ya bayyana cewa za a shiga gawar cikin gida kafin ayi mata sallah iyalansa su yi bankwana da shi.

A gefe guda kuma, sojojin da suke tafiyar da al’amuran kula da gawar sun kafe kai da fata cewa an ba su umarnin cewa kadda a tsaya da wannan gawa ko’ina sai inda za a yi mata sallah, bayan nuna bacin rai da Dikko Radda ya yi ne aka samu nasara sojojin suka bijirewa wancan umarni da aka ba su da farko suka bari aka shiga da gawar domin yin bankwana da ita

Kamar yadda na ce abubuwa da yawa sun faru wanda mutum daya ba zai iya lura da su ba shi kadai, idan za a tuntubi jama’a kowa zaka ji irin abubuwan da ya lura da su, da kuma irin darasin da yake ganin suna dauke da shi.

Wannan ke nan! Yanzu dai dai ana cigaba da yin tururuwa zuwa garin Daura domin ta’aziyyar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ga iyalan sa, ‘yan da kuma abokan arziki.

 

Yadda Aka Gudanar Da Jana’izar Buhari A Daura

An gudanar jana’izar marigayi tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke garin Daura cikin Jihar Katsina, a ranar Talatar da ta gabata, bayan tabbatar da rasuwarsa a ranar Lahadi a Landan.

Muhammadu Buhari dai ya rasu ne sakamakon ‘yar jinya da ya yi. Tsohon shugaban ya rasu yana shekara 82, kuma ya mutu ya bar ‘ya’ya 10.

 

Kwamitin shirya jana’zar

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin da ya jagoranci jana’izar tsohon shugaban kasar.

Kwamitin karkashin jagorancin Babban Sakaten Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya jagoranci shiryawa tare da tsara yadda za a gudanar da jana’izar.

Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnati, Segun Imohiosen ya fitar ya ce mambobin kwamitin sun hada da:

Ministan kudi, Ministan kasafi da tsare-tsare, Ministan Tsaro, Ministan yada labarai, Ministan ayyuka, Ministan cikin gida, Ministan Abuja, Ministan Gidaje da raya birane, Ministan kiwon lafiya, Ministar al’adu, Bai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Mai Bai bai wa shugaban kasa shawara kan tsare-tsare, Babban mai taimaka wa shugaba kan harkokin siyasa, Babban sifeton ‘yansanda, Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, da kuma Babban hafsan tsaron kasar.

 

Lokacin jana’izar

A ranar Talata ce aka yi jana’izar marigayi da misalin karfe 2:00 na rana a mahaifarsa ta Daura da ke Jihar Katsina.

Gwamnan Jihar ta Katsina, Dikko Radda, ne ya bayyana cewa gawar marigayin za ta bar birnin Landan da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Talata inda ake sa ran ta isa birnin Katsina da misalin karfe 12:00 na rana.

Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima tare da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne za su yi rakiyar gawar daga Landan zuwa Daura kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni.

Gwamnan na Katsina ya kuma bayar da tabbacin da ya samu daga shugaban Nijeriya, Bola Tinubu cewa shi da wasu shugabannin kasashe biyu za su halarci jana’izar da za a gudanar a mahaifar marigayin da ke Daura.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya tarbi gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Katsina, domin yi masa jana’iza a Daura.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris wanda ya tabbatar da hakan ya ce za a yi wa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura inda za a binne shi.

Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamiti na musamman da suka tsara jana’izar da kuma duk wani abu da ake bukata wajen binne shugaban.

 

Shugabannin duniya sun yi ta’aziyya

Firaministan India Narendra Modi ya shiga jerin shugabanni da kuma dimbim al’ummar da ke mika ta’aziyyarsu bisa rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na D a ranar Litinin, Modi ya jinjina wa kaifin basira da jajircewar marigayi tsohon shugaban kasar kan karfafa alakar Indiya da Nijeriya a lokacin mulkinsa.

Shi ma shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya bayyana mutuwar muhammadu Buhari a matsayin babban rashi .Daga nan ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan shugaban kasar da shugaba Tinubu da ma daukacin al’ummar Nijeriya baki daya.

Sai kuma kungiyar Tarayyar Afrika ta aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari ga iyalansa da gwamnatin Nijeriya.

 

Manyan bakin da suka hallara Jihar Katsina domin halartar jana’izar

Akwai Firaministan Kasar Nijar Ali Lamine Zeine da kuma ministan Kasafin Kudi da tsare-tsare na Nijeriya Sanata Abubakar Bagudu da ministan yada labarai Muhammad Idris da tsohon ministan sufuri Rotumi Ameachi da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare.

Sannan akwai tsohon mataimakin shugaban kasar Kuma jagoran ‘yan adawa Atiku Abubakar da Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Remi Tunubu da tsohon ministan shari’ar Abubakar Chika Malami da Sanata Abdul’azziz Yari.

Tsofaffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, shugabannin tsaro, sarakuna, da manyan kasashen waje sun tsaya kafada da kafada cikin girmamawa. Sunaye irin su mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, hamshakin attajirin masana’antu Aliko Dangote, mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, Ibrahim Masari, Ibrahim Gambari, tsohon shugaban kasar Nijar Muhammadu Yusufu, da dai sauransu sun nuna haduwar tasu a tsawon shekaru da dama.

Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, tsohon ministan sadarwa Isa Ali Pantami, Sanata Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan Jihar Kebbi Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan Ekiti Kayode Fayemi, da na Katsina Aminu Bello Masari duk sun hallara. Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, sun tare a tawagar da ke nuna girman tasirin siyasar Buhari.

 

Yadda Tinubu Ya Karbi Gawar Cikin Karramawar Soja

A ranar Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina.

Shugaba Tinubu ya isa filin jirgin ne daga Abuja da karfe 1:42 na rana, sannan ya duba jami’an tsaro kafin jirgin saman Nijeriya dauke da gawar marigayin ya sauka da misalin karfe 1:51 na rana.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, uwargidan shugaba Buhari Aisha, da sauran ‘yan uwa ne suka raka gawar shugaba Buhari zuwa Nijeriya.

Shugaba Tinubu, tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban kasar Guinea-Bissau Umaru Sissoco Embaló, firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, tsohon shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou, da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne suka karbi akwatin gawar marigayi shugaban kasar daga jirgin.

Tawagar hadin gwiwar jami’an tsaro na soja da suka hada da manyan hafsoshi tara ne suka ajiye gawar wadda aka lullube da tutar Nijeriya a kan wata motar daukar gawa. Tawagar ta hada da Manjo-Janar Mohammed Usman, Manjo-Janar Oluwafemi Williams, Manjo-Janar Shuaibu Nuhu, Rear Admiral Suleiman Dahun, Rear Admiral Jonathan Ajodo, Rear Admiral Samuel Ngatuwa, Air Bice Marshal Adeniyi Herbert Amesinlola, Air Bice Marshal Idi Sanni, da Air Bice Marshal Obinna Obiabaka. Manjo Janar Mike Alechenu ne ya jagoranci tawagar.

 

Atiku

Atiku: Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjina wa marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin “daya daga cikin manyan ‘ya’yan Nijeriya” kuma shugaban da ya dauki nauyin bautar kasa da jajircewa.

Atiku ya kara da cewa, “Abin alfahari ne kasancewa a Daura, mu tsaya kafada da kafada da iyalansa, da ‘yan uwansa, da al’ummar Nijeriya yayin da muka mika shi ga zuwa makwancinsa.”

 

Amurka

A kasar Amurka, inda Nijeriya ke kwaikwayon tsarinta na shugaban kasa, rasuwar tsohon shugaban kasa ya kasance wani babban biki ne mai matukar muhimmanci, inda duk tsofaffin shuwagabannin jam’iyyu masu rai a fadin jam’iyyu ke haduwa cikin hadin kai domin karrama wadanda suka rasu.

 

Matthew Hassan Kukah

Limamin cocin Katolika na Diocese na Sakkwato, Matthew Hassan Kukah, a nasa jawabin, ya ce marigayi tsohon shugaban kasa mutum ne nagari wanda ya kamata a yi la’akari da kimarsa da ayyukan da ya gabatar a shugabancinsa na tsawon shekaru takwas.

Wannan kalamai na karramawar Kukah sun zo ne a daidai lokacin da Sarkin Musulmi Alhaji Mohammed Sa’ad Abubakar na Uku ya gabtar da nasa jawabin, inda ya bayyana Buhari a matsayin shugaban da ya zo, kuma ya ci nasara.

 

Gibin da rasuwar muhammadu buhari za ta samar a siyasar nijeriya

Rasuwar tsohon shugaban babu shakka ta samar da gibi a siyasar Nijeriya musamman a arewacin kasar.

Masu fashin baki na ganin rasuwar tsohon shugaban kasar ka iya haifar da wani kokari daga ‘yan siyasar arewacin kasar na maye gurbinsa musamman a daidai lokacin da zaben shugaban kasa na 2027 ke kara karatowa.

A yankin arewacin kasar ana kallon Muhammadu Buhari ba kawai a matsayin dan siyasa ba har ma da kasancewarsa mahada tsakanin talakawa da masu fada a ji.

Mutum ne da yake da mabiya na ga-ni-kashe ni a yankunan karkara da biranen yankin arewacin Nijeriya.

Kimar da yake da ita a zukatan talakawa ta sa shi ne mutum daya tilo da yake iya samun miliyoyin kuri’u a takararsa a 2011 inda ya samu kuri’a miliyan 12 musamman daga arewacin kasar.

Buhari ne dan siyasar da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2015 a jam’iyyar APC ta hadaka kuma ya samu nasarar lashe zaben da yawan kuri’u miliyan 15.4, bayan bai wa shugaba mai ci, Goodluck Jonathan tazarar kuri’u fiye da miliyan 2.5.

Kuma wannan nasara ta sake fito da kimar da Buhari yake da ita a matsayin dan siyasa mafi karfi a Nijeriya.

 

Farfesa Khalid Aliyu, Sakatare Janar na Jama’atu Nasril Islam, JNI

Wasu daga cikin kalaman da ya yi a lokacin rantsuwarsa ta kama aiki da suka kada hantar masu fada a ji a kasar sun hada da “Ni ba na kowa ba ne, kuma ni na kowa ne.”

“Kalamansa sun girgiza masu fada a ji abin da ya janyo da dama daga cikinsu suka fice suka bar kasar,” in ji shi,”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Raya Hulda Tsakanin Sin Da Australia Ya Dace Da Yanayin Zamanin Da Ake Ciki

Next Post

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

Related

Natasha Ta Rubuta Wa Majalisa, Tana Neman A Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu
Manyan Labarai

Natasha Ta Rubuta Wa Majalisa, Tana Neman A Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu

12 hours ago
Babu Wata Sabuwar Ƙungiyar  Ƴan Ta’adda Mai Suna Fethulla A Nijeriya – DHQ
Tsaro

Babu Wata Sabuwar Ƙungiyar  Ƴan Ta’adda Mai Suna Fethulla A Nijeriya – DHQ

15 hours ago
Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato

18 hours ago
Dele Momodu Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC
Manyan Labarai

Dele Momodu Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC

22 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Yaƙi Da Masu Damfara A Intanet
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Yaƙi Da Masu Damfara A Intanet

1 day ago
Buhari Ya Taimake Ni Lokacin Da Wasu Ke Ƙoƙarin Ruguza Majalisar Tarayya — Gbajabiamila
Manyan Labarai

Buhari Ya Taimake Ni Lokacin Da Wasu Ke Ƙoƙarin Ruguza Majalisar Tarayya — Gbajabiamila

1 day ago
Next Post
Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

LABARAI MASU NASABA

yola

Tinubu Ya Kammala Hanyoyi 420 A Sassan Nijeriya Cikin Shekara 2

July 18, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare

Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare

July 18, 2025
Manzon Allah

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (3)

July 18, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Manyan Jami’an ‘Yansanda 150 Ke Fuskantar Kwamitin Ladabtarwa

July 18, 2025
Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

July 18, 2025
Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya

Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya

July 18, 2025
Raya Hulda Tsakanin Sin Da Australia Ya Dace Da Yanayin Zamanin Da Ake Ciki

Raya Hulda Tsakanin Sin Da Australia Ya Dace Da Yanayin Zamanin Da Ake Ciki

July 17, 2025
Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Kano Don Ta’aziyyar Ɗantata

Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Kano Don Ta’aziyyar Ɗantata

July 17, 2025
Gudummawar Sin Ga Tattaunawa Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai Da Dunkulewar Duniya

Gudummawar Sin Ga Tattaunawa Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai Da Dunkulewar Duniya

July 17, 2025
Natasha Ta Rubuta Wa Majalisa, Tana Neman A Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu

Natasha Ta Rubuta Wa Majalisa, Tana Neman A Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu

July 17, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.