Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar baya tunanin neman wa’adi na uku na mulki, saboda haka a shirye ya ke ya bayar da mulki da zarar wa’adin sa ya kare a shekara mai zuwa.
Buhari yayi wannan jawabi ne a lokacin da yake magana da Fira ministan Birtaniya Boris Johnson a wajen taron kasashe rainon Ingila da yake gudana a kasar Rwanda.
Shugaba Buhari yace tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da yayi kokarin yin tazarcen bai samu nasara ba.
Tun da farko dai Boris Johnson ne ya tambayi Buhari ko zai tsaya takara domin neman wa’adi na uku nan take Buhari ya ce bashi da niyyar yin hakan.
A ranar 29 ga watan Mayun shekara mai zuwa ne Buhari zai mika mulki ga zababben shugaban kasar da ‘yan Najeriya za su zaba domin maye gurbinsa, bayan kammala wa’adin sa na biyu.