Kungiyar Manoma ta Ƙasa reshen jihar Katsina AFAN, ta bayyana tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari a matsayin wani gwarzo wanda tsare-tsaren gwamnatin sa ne suka fito da ƙima da kuma martabar manoma a Nijeriya.
Shugaban Kungiyar a jihar Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kaiwa tsohon shugaban Kasar ziyarar ban girma a gidansa da ke Daura.
A cewarsa, tsare-tsaren da gwamnatin shugaba Buhari ta zo da su a ɓangaren noma sun taimaka matuƙa musamman yadda kananan manoma suka amfana da tsarin, sabida haka ne manoma yanzun suka zama kamar wasu sarakai.
Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya ce duk wani manomi a ƙasar nan yana cikin rufin asiri, sai dai ba mai gane wannan kokari da shugaba Buhari ya yi sai mai hankali da tunani zai gane tasirin tsare-tsaren gwamnatinsa a harkar noma.
Haka kuma, ya bayyana cewa a baya, jihar Katsina babu injinan casar shinkafa, yanzu kuwa har katafaran kamfanin casar shinkafa akwai wanda shi shugaban ƙasa ya bude da kansa, kuma yana samar da shinkafa yadda ya kamata a jihar Katsina da wasu jihohin Nijeriya.
Hon. Ya’u Umar wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar na jihar ya bayyana dalilin kawo wannan ziyara, inda ya ce sun zo ne akan batutuwa masu muhimmanci guda biyu.
‘Mai girma tsohon shugaban Kasa, mun zo tayaka murna ka gama mulki lafiya ka dawo gida, lallai muna yi wa Allah godiya akan wannan ni’ima da ya yi mana na samunka a matsayin shugaban ƙasa wanda ya san ciwon manoma ‘ inji Gwajo-Gwajo
Shugaban kungiyar ya ƙara da cewa batu na biyu da ya kawo su shi ne, neman shawara da neman albarka ga tsohon shugaban ƙasar musamman abubuwan da suka shafi yadda za su ƙara inganta harkokin noma da kiwo a wannan yanki na arewa.