Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Hon Ndudi Elumelu, ya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaji, ya kara da cewa, kamata ya yi a kyale shi ya koma kauyensu.
Elumelu, ya shaida hakan ne a lokacin da wasu ‘yan Majalisun PDP suka ziyarci ofishin tsohon mamba na Jam’iyyar APC, Daniel Bwala, a Abuja.
- Ya Kamata Makusanta Buhari Su Ba Shi Shawarar Yin Murabus —Hakeem
- Da Dumi-Dumi: Sanatoci Sun Lashi Takobin Tsige Buhari Saboda Matsalar Tsaro
Sauran ‘yan Majalisun da suka halarci taron ficewar Bwala daga APC sun hada da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Hon. Tobi Okechukwu, mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar, Hon Adesegun Adekoya Abdul-Majid da wasu tara.
Elumelu ya jinjina wa Bwala bisa fice wa daga APC bayan gano gazawarta, “Na ji Sanatoci na yunkurin tsige Buhari. Muma za mu bibiyi batun. Zan kuma sanar da matsayarmu nan kusa. Saboda mutumin da ake magana a kansa ya gaji, me yesa zai ci gaba da zama a kujerar Shugaban kasa? Ya gaji. Kamatuwa ya yi a bukace shi da ya koma kauyensa kawai. Wannan shi ne tunani mai kyau.”
Daga bisani ya bukaci Bwala da ya shiga cikin jam’iyyar PDP domin ceto Nijeriya daga halin da take ciki, ya kara da cewa APC ta ruguza abubuwa a kasar nan.
Ya soki Gwamnatin APC bisa gaza shawo kan yajin aikin ASUU tare da cewa kashe-kashen rayuka da ake yi a kasar nan kawai ya isa al’umma su yanke kauna daga APC, “ka duba abubuwan da suke faruwa a kasar nan yanzu. Muna bukatar hada karfi da karfe domin ceto kasar nan.”