Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika lambar yabo ta kasa ‘Member of the Federal Republic’ (MFR) ga wakilan gidan Talabijin na kasa (NTA) da suke dauka da aikewa da rahotonni daga fadar shugaban kasa, tare da mai dauka masa hoto na kashin kai, Bayo Omoboriowo.Â
Wadanda suka amshi lambar yabo ta kasa daga NTA din sun hada da Adamu Sambo da Emmanuel Anrihi.
Mutanen wadanda suka kasance masu daukowa da yada ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara takwas da ya yi a mulki. Ya ba su lambar yabon ne da zimmar nuna godiya ga hidimtawa da suka yi tare da kokarinsu da jajircewarsu a bangaren aiki.
Kazalika, mai daukan hoto wa mataimakin shugaban kasa, Tolani Alli shi ma ya samu lambar yabon kasa ya MFR.
Har-ila-yau, Sunny Aghaeze, shi ne ma dauka wa shugaban kasa hoto, da Tolu Ogunlesi, mai taimaka wa shugaban kasa kan fasahar sadarwar zamani da sabbin kafafen sadarwa (SA) sun samu lambar yabon kasa ta ‘Member of the Order of Niger’ (MON).
A wani mataki na nuna godiya ga hidimarsu da ayyukansu, shugaba Buhari ya mika lambar yabo ta kasa ga kusan dukkanin mashawartansa na musamman da masu taimakansa da ke aiki a ofishinsa da kuma ofishin mataimakin shugaban kasa.