Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugabanni da wasu manyan mukamai na makarantun gwamnatin tarayya guda uku a kasar nan.
Sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar a ranar Laraba, mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Ben Goong, ta ce nadin shugabannin ukun, yana da wa’adi na shekara biyar kowanne a ofis, daga ranar 17 ga Janairu, 2023.
Shugabannin da makarantunsu, sune; Dakta Paul-Darlington Ndubuisi, Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Tarayya, Isuochi, Jihar Abia; Farfesa Mohammed Magaji, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo, Jihar Kano da Dakta Duke Okoro, kwalejin Kimiyya da fasaha ta tarayya, Orogun, Jihar Delta.
Har ila yau, shugaban ya amince da nadin magatakarda gasu kamar haka: Umar Dumbulum, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo Jihar Kano; Christine Aluyi, Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Orogun, Jihar Delta da Ezenuruihe Olachi, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Isuochi, Jihar Abia.