Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Ƙasa (NIS), Idris Isah Jere, zuwa ƙarshen wa’adin mulkinsa da zai kasance ranar 29 ga Mayun 2023.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, Tony Akuneme ta bayyana cewa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya tabbatar da ƙarin wa’adin ga shugaban na NIS, a wata takarda da ya rattaba wa hannu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni CGI Idris Isah Jere ya ci gaba da aiki a shalkwatar hukumar ta NIS da ke Abuja.
28th April 2023
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp