Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya ziyarar aiki daga ranar Talata 11 zuwa 19 ga watan Afrilu a ziyararsa ta karshe zuwa kasar a matsayin shugaban kasa.
Haka kuma zai yi amfani da damar wajen gudanar da aikin Umrah.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce shugaban zai samu rakiyar wasu daga cikin mukarrabansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp