Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Amurka gobe Lahadi don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da za agudanar a birnin New York.
Mataimakin shugaban kasa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Tuwita.
Bashir Ahmad, ya ce shugaban zai gabatar da jawabi a ranar Laraba a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp