• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bunkasar Cinikin Waje Ta Kasar Sin Ta Wuce Zaton Mutane

by CMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana yau Talata cewa, darajar kayayyakin da kasar ta sayar zuwa ketare a watan Afrilun bana ta kai kudin Sin RMB yuan traliyan 2.02, wadda ta karu da 16.8% bisa na makamancin lokacin bara. Bunkasar darajar kayayyakin da kasar Sin ta sayar zuwa ketare a watan Afrilu ta sake wuce zaton mutane.

Kamfanin dillancin labaru na AP ya ruwaito cewa, ko da yake bukatun da ke akwai a duniya sun yi rauni, amma kasar Sin ta yi fice wajen sayar da kaya zuwa ketare.

  • Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Nadin Sarautar Sarki Charles III

Me ya sa hakan? Saboda gwamnatin kasar Sin ta dade tana kara azama kan manufarta ta bude kofarta ga ketare, da fitar da matakan tabbatar da kwanciyar hankali a cinikin waje.

Tun daga farkon shekarar bana ne hukumomin sassan kasar Sin suka dauki matakan sa kaimi kan bunkasuwar cinikin waje, kana kamfanonin kasar Sin sun je ketare domin neman kwangiloli.

A karshen watan Afrilu kuma, gwamnatin Sin ta fitar da wasu sabbin matakai, ciki had da maido da shirya shagulgula a zahiri a gida, shirya tattaunawa tsakanin kamfanonin kera motoci da kamfanonin jigilar kaya cikin jiragen ruwa, da goyon bayan kamfanonin cinikin waje su yi ciniki ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa da kuma habaka hanyoyin sayar da kayayyaki. Dukkan matakan suna da amfani da dacewa, tare da samarwa kamfanonin cinikin waje sabbin damammakin ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

An yi imanin cewa, sakamakon gudanar da shagulgula da dama a gida, da kara saukaka yin mu’amala a tsakanin mutane, da kuma rika yin kirkire-kirkire a harkokin ciniki, kasar Sin za ta samu karin kuzari kan raya cinikin waje, kuma za ta kara aikewa duniya alamar saurin farfadowar tattalin arzikinta. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha
Daga Birnin Sin

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
Next Post
Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2, Sun Kwato Makamai A Anambra

Jami'an Tsaro Sun Kashe Mahara 2, Sun Kwato Makamai A Anambra

LABARAI MASU NASABA

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.