Cikin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 15 da kasar Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2026 zuwa ta 2030, an tsara bunkasa fannin kirkire-kirkiren fasaha, a matsayin matakin ingiza ci gaba mai nagarta. Wannan ci gaba zai taka rawar gani wajen kara raya tattalin arzikin Sin, da ma amfanar da sauran sassan kasa da kasa.
Wasu sassa na ganin ci gaban kasar Sin ba mai dorewa ba ne, yayin da wasu bangarorin musamman na yammacin duniya ke ganin bunkasar Sin na iya dakushe nasu ci gaban. To sai dai kuma inda mun yi nazari sosai, za mu ga dukkanin wadannan ra’ayoyi biyu kuskure ne, domin kuwa bunkasar kasar Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohi, zai ingiza ci gaban sauran sassan kasa da kasa ne ba wai haifar da wata matsala ba.
- Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda
- Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
Dalilin a kan haka shi ne alal misali, cikin shirin raya kasa na shekaru biyar masu zuwa, an tanadi aiwatar da matakai na ingiza bude kofa bisa matsayin koli, da samar da sabon yanayi na cimma moriyar juna tsakanin Sin da sauran sassan kasa da kasa.
Bugu da kari, shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa alakar ci gaban kirkire-kirkiren fasahohin Sin da sauran sassan duniya, ya kunshi kafa tushe na samar da karin daidaito a fannoni da dama, ciki har da hada-hadar cinikayya ta dijital, da ilimi da jagoranci.
Ta hanyar rage gibin dake akwai tsakanin mabanbantan sassan duniya, sashen kirkire-kirkiren fasahohin Sin na kara fadada damar raya masana’antun duniya, da samar da guraben ayyukan yi, musamman a yankunan duniya da aka jima da yin watsi da su, wanda hakan zai yi matukar amfanar da tsarin kasuwancin duniya.
A fannin raya fasahohin cin gajiyar makamashi marar dumama yanayi ma kasar Sin na kara taka rawar gani, inda alal misali Sin ke bayar da babbar gudummawa ga babban burin nahiyar Turai na fadada amfani da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa, wani mataki da a halin da ake ciki ke kara ingiza aniyar manyan kamfanonin kera batira na kasar Sin, su zuba jari a kamfanonin kirar ababen hawa masu amfani da lantarki na Turai, irin su kamfanonin dake kasashen Jamus, da Faransa da Hungary.
Ta haka, kamfanonin Turai za su ci karin gajiyar fasahohin Sin na kera batiran ababen hawa, da ingiza saurin ci gaban fasahohin da kamfanonin na Turai ke bukata a wannan fage.
Ko shakka babu, ta hanyar samar da kyakkyawan yanayin bude kofa ne kadai, gajiyar kirkire-kirkiren fasahohin kimiyya da fasaha tsakanin sassan kasa da kasa za su amfani duniya baki daya. Musamman duba da cewa, tattalin arzikin duniya ba wai wani abu ne guda daya da wasu za su ci gajiyarsa wasu kuma su rasa ba, maimakon haka, wani tsari ne mai sassauyawa wanda a cikinsa tsarin gudanar kirkire-kirkiren fasahohi ke iya fadada damar dukkanin sassan duniya ta cin gajiya marar iyaka.














