Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga.
Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi.
- Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
- Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi.
Yanzu za a jira daya kungiyar daga Championship domin sanin wadanda zasu buga gasar Firimiya a badi, hakazalika za a jira kungiya daya da zata koma gasar yan dagaji daga Firimiyar.