Shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC), Mista Hussaini Magaji, ya bayyana dalilan da ke sa yawanci harkokin kasuwanci da kamfanoni da aka kafa suke durkushewa a fadin kasar nan.
Mista Magaji Hsussain ya bayyana haka ne a taron kwana daya da hukumar ta shirya wa manyan ma’aikatanta a garin Keffi ta Jihar Nasarawa. Magaji wanda ya samu wakilcin wata babbar darakta a hukumar mai suna, Justine Nidia, ya ce, yawancin harkokin kasuwanci a Nijeriya na kasa kai labari ne saboda rashin samar da tsari da kuma rashin iya tafiyar da harkokin kasuwancin.
- Jarin Waje Na Kai Tsaye Dake Shigowa Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 1.04 Cikin Watanni 11 Na Farkon Bana
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
Ya kuma kara da cewa, “Kididdigar da ke a hannunmu ya nuna cewa, kashi 20 na harkokin kasuwancin da aka kirikro suna durkushewa ne a cikin shekara 2 na farko, kashi 45 kuma suna durkushewa a cikin shekara 5 na farko yayin da kuma kashi 65 na kamfanonin da aka bude ke mutuwa a cikin shekara 10 na farko.
“Kashi 25 na harkokin kasuwanci ke iya kaiwa shekara 15 zuwa sama. Wannan kuma yana faruwa ne saboda rauni wajen samar da tsarin tafiyar da kamfanin da kuma rashin iya gudanarwa. A kan haka ya jaddada cewa, domin tabbatar da ci gaba dole hukumar ta shiga sahun fadakarwa a kan yadda za a rika gudanar da harkokin kamfanoni don a rage yadda suke mutuwa.”
Ya kuma kara da cewa, hukumar CAC za ta saukaka hanyoyin yi wa kamfanoni rajista tare da basu tallafi don ganin sun zama manyan kamfanoni a nan gaba.