Gabanin fara wasannin ƙasashen Afrika na ƙwallon ƙafa ta mata da hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta shirya a ƙasar Morocco da za a fara a ranar Asabar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) za ta ƙaddamar da sabon kofin gasar a wani ɓangare na ƙoƙarin ɗaukaka wasan ƙwallon ƙafa na mata a nahiyar Afrika.
A ranar Laraba, 02 ga watan Yuli na shekarar 2025 za a ƙaddamar da sabon kofin gasar cin kofin Afrika ta mata a ƙasar Morocco, ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta bana, sabon kofin wani ɓangaren ne na burin shugaban CAF Dr Patrice Motsepe na bunƙasa ƙwallon ƙafa na mata a Afrika.
- NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano
- An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani
CAF za ta ƙaddamar da kofin a shafukanta na sada zumunta sannan kuma a wani taron da ta shirya gudanarwa tare da masu ɗaukar nauyin gasar ta bana, a ranar Asabar 05 ga Yuli, 2025 za a fara gasar cin kofin Afrika ta mata, a filin wasa na Olympic da ke Rabat yayinda da masu masaukin baƙi, Morocco za ta karawa da Zambia.
Ranar Lahadi 6 ga watan Yuli Nijeriya za ta kece raini da ƙasar Tunisia a wasan rukunin B a filin wasa na Larbi Zaouli dake birnin Casablanca na ƙasar Moroko da misalin karfe 4 na yamma Agogon Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin koci Justin Madugu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp