Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ‘yan kasar nan marasa kishi ke sayar da sabbin takardun kudi.
CBN ya kuma bayyana takaicinsa kan wadanda ke cin zarafin takardun Naira ta hanyar yi liki a wajen shagalin biki.
- Sin Ta Tallafawa Makarantun Sudan Ta Kudu Da Litattafai Sama Da 300,000
- Hisbah Ta Wanke Matar Da Ta Auri Saurayin ‘Yarta A Jihar Kano
A cikin sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwasinobi, ya fitar a yau Alhamis, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ake samun layuka a wajen injin ATM a daukacin fadin kasar nan.
Har ila yau, CBN ya bayyana takaici kan yadda wasu ma’aikatan bankuna ke sauya al’ummar gari tsofaffin takardun kudaden da sabbin kudaden ta hanyar bayan fage, inda bankin ya gargade su cewar hakan ya saba wa doka.
Sanarwar ta kara da cewa, CBN na son ya sanar da wadanda ke sayar da sabbin takardun kudi ko kuma yin liki a wuraren bukukuwa, karya doka ne.
A cewar CBN, sashe na 213 na dokar CBN da aka sabunta, ta haramta yin likin kudi a dukkanin wuraren taro.
Sanarwar ta kara da cewa, har ila yau, sashe na 214 ya bayar da damar a hukunta duk wanda ya yake sayar da kudin kasar nan.
CBN ya ce, ya yi hadaka da ‘yansanda da hukumar EFCC da kuma hukumar da ke sa ido a kan hada-hadar kudi (NFIU) domin kama duk wanda ya yake sayar da kudin.
Bankin ya kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin wadata bankunan kasar. An da sabbin takardun kudaden.