Babban Bankin Nijeriya ya dage takunkumin ajiye kudi adadin Dala 10,000 asusun ajiya ne a wani bangare na gyaran fuska kan harkokin Bankin.
Bankin ya ce, masu asusun suna da ‘yancin ziyartar asusunsu a kowanne lokaci ba tare da kayyadewa ba.
Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan wani taro da kwamitin ma’aikatan bankuna a ranar Lahadi.
An yi taron ne don ba da kwarin guiwa ga masu asusun Dala, kan sauye-sauye da Babban Bankin ya yi a kasuwar ‘yan canji na baya-bayan nan da kuma tattaunawa da aiwatarwa da kuma tasirin sauye-sauyen manufofin ga abokan huldar bankuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp