Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kara kudin ruwa da kashi 18.75 daga kashi 18.5, wanda wannan ne kudin ruwa mafi tsada da aka taba samu a cikin shekara 22.
Mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi ne ya bayyana karin a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan taron kwamitin tsare-tsaren harkokin kudade na kwanaki biyu da ya gudana a Abuja.
Wannan ita ce ganawa ta farko na kwamitin tsare-tsaren harkokin kudade da mukaddashin gwamnan na CBN ya jagoranta tun bayan dakatar da tsohon gwamnan, Godwin Emefiele.
Haka kuma wannan shi ne karon farko da kwamitin tsare-tsaren harkokin kudade ya fara ganawa a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp