Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa, zai kakabawa Bakununan Kasuwanci na kasar tarar Naira miliyan 150, idan aka same su suna taimakawa wajen sayar da sabbin takardun kudade.
Kazalika, Bankin na CBN, ya kuma sanar da cewa, zai hukunta ‘yan koren wadannan bankunan da ke sayar da sabbin takardun kudin.
- Mun Karbi Rancen Dala Biliyan 1 Don Tallafa Wa Matatar Man Dangote —NNPC
- Wolves Ta Naɗa Vitor Pereira A Matsayin Sabon Kocinta
Mukaddashin riko na sashen gudanar da ayyuka na Bankin Solaja Mohammed J. ya sanar da haka a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Disambar 2024 waccw kuma take dauke da lamba kamar haka; COD/DIR/INT/CIR/001/025.
Wannan takardar, na daga cikin sake maimacin gargadin da Bankin na CBN ya fitar a ranar 13 ga watan Nuwumbar 2024
Kazalika, Bankin ya nuna bacin ransa kan yadda ake ci gaba da sayar da sabbin takardun kudaden
Bankin na CBN ya ci gaba da cewa, sayar da sabbin takardun kudaden na janyo karancin sabbin kudaden a hannun alummar kasar.
CBN ya kara da cewa, wannan halin na sayar da sabbin takardun kudaden kasar, zai iya yiwa tattalin azrkin Nijeriya illa da kuma zubar da kimar kasar tsarin kula da kudaden kasar.
Takardar ta sanar da cewa, Bankin na CBN ya kara zage damtse wajen bibiyar ayyukan da ake gudanar a cikin Bankunan kasar da kuma a wajen injinan cire kudi na ATM, domin duba yawan kudaden da abokan hudda da bankuna suka cire, musamman domin a bankado da irin wadannan mutanen masu sayar da sabbin takardun kudaden, a daukacin fadin Nijeriya.
A cewar takardar, duk Bankin da da Babban Bankin na CBN ya kama da aikta wannan harkallar, za a hukunta shi ciki har da cin su tarar kudi ta Naira miliyan 150.
Bankin ya ci gaba da cewa, akwai doka ta(BOFIA) 2020 da aka tanada domin hukunta duk wanda aka kama yana aikata wannan harkallar.
Wani jami’i a Bankin na CBN da bai bukaci a bayyana sunan sa ba, ya sanar da cewa, wannan matakin da Bankin ya yanke na hukunta duk wanda aka kama yana yin wannan harkallar, za ta dakushe kwarin guiwar masu sayar da sabbin takardun kudaden kasar.
A cewarsa, mun mayar da hankali wajen ganin ana bai wa tkardun kudin kasar kimar da suke da ita.
A bisa haka ne, Babban Bankin ya umarci daukacin Bankunan kasar da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade da su tabbatar da ana bin ka’ida hada-hadar kudade a rassan su.
A cewar Babban Bankin na CBN, wadannan matakan na da matukar mahimmanci, musamman domin a samu takardun kudaden, suna zagayawa a hanun jama’a yadda ya kamata.
Kazalika, wani ma’aikacin banki da bai bukaci a bayyana sunan sa ba, ya tabbatar da wannan umarnin da Bankin na CBN, ya umarci Bankunan da kuma cibiyoyin hada-hadar kudi.
Ya yabawa Bankin na CBN, bisa daukar wannan matakan, inda ya bayyana cewa, akwai kuma bukatar Bankunan kasar, su goyi bayan matakan na Bankin CBN.
Wannan makain na Bankin CBN na daya daga cikin matakan Bankin na kokarin tsarkake gudanar da ayyukan Bankunan kasar da kuma cibiyoyin hada-hadar kudi.