Jiya ne kamfanin China Habor Engineering Ltd, CHEC a takaice, ya mikawa gwamnatin kasar Najeriya Lekki, tashar teku mai zurfi ta farko ta kasar, bayan nasarar kammala katafaren aikin tashar jiragen ruwa da ya yi a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.
Jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana a yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tashar za ta biya bukatun raya tattalin arzikin Najeriya.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana a yayin bikin cewa, sabuwar tashar jiragen ruwan, za ta sanya Lagos a matsayin cibiyar hada-hadar sufurin ruwan ba kawai a yammacin Afirka ba, har ma a yankin tsakiya da yammacin Afirka baki daya.
Tashar teku mai zurfi da kamfanin CHEC ya gina, ita ce tashar ruwa mafi girma a Najeriya, kana daya daga cikin mafiya girma a yammacin Afirka.
An dai fara aikin gina tashar ce a watan Yunin shekarar 2020, an kuma tsara tashar ta yadda za ta iya sarrafa kwantenoni miliyan 1.2 a shekara. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)