Sabon kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya fara aikin sa da nasara, bayan da tawagar ta doke ƙasar Rwanda da ci 2-0 a filin wasa na Amahoro.
Chelle ya karɓi ragamar horar da Super Eagles watanni biyu da suka gabata, kuma wannan shi ne wasan farko da ya jagoranta.
- El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
- Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i
Wannan wasa na cikin zagaye na biyar na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a shekarar 2026.
A halin yanzu, Nijeriya na matsayi na huɗu a rukuni C da maki 6 bayan buga wasanni biyar.
Afirka Ta Kudu ce ke jan ragama, Benin na matsayi na biyu, yayin da Rwanda ke matsayi na uku.
Victor Osimhen ne ya ci wa Nijeriya duka ƙwallayen biyu a wasan, tare da taimakon Ademola Lookman da Samuel Chukwueze.