Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan Ingila mai shekaru 20, Jamie Gittens daga Borussia Dortmund kan kuɗi fan miliyan 48.5, tare da yiwuwar ƙarin fan miliyan 3.5 idan ya taka rawar gani.
Gittens, wanda ya koma Dortmund daga Manchester City a shekarar 2020, ya zura ƙwallaye 17 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 14 a wasanni 107 da ya bugawa ƙungiyar Jamus ɗin. Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru bakwai a Stamford Bridge, wanda zai kai shi har zuwa 2032.
Chelsea ta ci gaba da sayen sabbin ‘yan wasa a wannan bazarar domin ƙarfafa tawagarta, inda Gittens ya shiga jerin sababbin ‘yan wasan da suka haɗa da ɗan wasan gaba na Ipswich Town, Liam Delap, dan wasan gaba na Brighton & Hove Albion, João Pedro, ɗan wasan tsakiya na Sporting, Dario Essugo, da mai tsaron bayan Strasbourg, Mamadou Sarr.
Gittens ya bayyana farin cikinsa da wannan sabon mataki, yana mai cewa, “Abin mamaki ne yanzu da na ganni a Stamford Bridge a matsayin ɗan wasan Chelsea. Babban abin alfahari ne kasancewa ta anan, kuma ina fatan rubuta nawa tarihin a wannan babbar ƙungiya ta Chelsea.”
Borussia Dortmund ta tabbatar da amincewa da yarjejeniyar a ranar Alhamis, inda darektan wasanni Sebastien Kehl ya ce tattaunawa da Chelsea ta kasance cikin sauki, kuma duka ƙungiyoyin biyu sun amince da wannan ciniki. Dortmund ta yiwa Gittens fatan alheri a sabon matakin da ya ɗauka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp