Kasar Sin tana gudanar da bikin baje kolin sabbin fasahohin zamani na kasa da kasa karo na 26 wato CHINA HI-TECH FAIR a takaice daga ranar 14 zuwa ta 16 a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, inda shahararrun kamfanoni da kungiyoyin kasa da kasa fiye da dubu 5 daga kasashe da yankunan sama da 100 suka halarta, kana kuma za a kaddamar da fasahohi, kayayyaki da sakamako sabbi fiye da 4300.
Tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu, an samu nasarar gudanar da bikin na CHINA HI-TECH FAIR sau 25, wanda yake matsayin muhimmin dandalin bude kofar kasar Sin ta fannin sabbin fasahohin zamani da kuma yin mu’amala da cinikin fasahohin zamani sabbi. (Tasallah Yuan)