Hukumar hana amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni ta kasar Sin (CHINADA) ta bayyana rashin amincewarta da gasar wasannin motsa jiki da aka sauya da mummunan sabon salo, wacce ke bai wa ‘yan wasa damar amfani da kwayoyi masu kara kuzari.
Gasar wacce aka shirya gudanarwa a watan Mayun shekarar 2026 a Las Vegas ta kasar Amurka, an yi Allah wadai da ita, a matsayin wacce za a kalla mai hatsarin gaske da ke barazana ga rushe asalin kyakkyawan tubalin da aka gina wasanni da walwalar ‘yan wasa a kai.
A cikin sanarwar da ta fitar a jiya Jumma’a, CHINADA ta yi tir da gasar a matsayin “karkatacciya da ke mayar da tsantsar gasar wasannin motsa jiki zuwa gasar shan kwayoyi, wadda ta saba wa manufar dokar hana shan kwayoyin kara kuzari a wasanni ta duniya.”
Hukumar ta CHINADA ta kara da cewa, “Gasar tana matukar yin barazana ga lafiyar jiki da kaifin tunani da basira na ‘yan wasa da kuma asalin ruhin wasanni. Bugu da kari, dabarun da aka bullo da su na yayata gasar ta tona asirin yanayinta a matsayin wani shiri na zuba jari don cin riba.”
Kazalika, hukumar ta ce, masu shirya wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzarin suna janyo hankulan ‘yan wasa ta hanyar sanya manyan kyaututtuka domin ingiza su, su yi kasada da kiwon lafiyarsu da kuma gamsar da sha’awar mutane na kallon wasan da ya kunshi “fafatawa ta kisan gilla”.
Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp