Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron tattauna ci gaban kasa da kasa jiya da yamma ta kafar bidiyo.
Cikin jawabin bude taron, Xi Jinping ya bayar da labarinsa na kasancewa manomi a wani karamin kauye dake yankin tsaunikan Loess na kasar Sin a karshen shekarun 1960.
Wannan labari na shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, ba tare da la’akari da inda suke ba, burin daukacin mutane shi ne samun ingantacciyar rayuwa.
Ga shugabanni kuwa, ci gaba da raya kasa ne kadai zai iya cimma burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa da zaman lafiyar al’umma. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp