Jimilar jami’an kasashe 45 abokan huldar kasar Sin karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da na kungiyar Tarayyar Afrika (AU), sun fara karbar horon dake mayar da hankali kan yaki da talauci, wanda ke gudana a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta daga ranar 19 zuwa 26 ga watan Oktoba.
Bayanai sun nuna cewa, nahiyar Afrika ce mafi fama da talauci a duniya, inda kasashe 23 cikin 28 mafiya talauci ke nahiyar, lamarin da ya sa ta mamaye sama da kaso 30 cikin dari na adadin masu fama da talauci na duniya. A daya hannu kuma, kasar Sin ce wadda ta gabatarwa duniya wani abun al’ajabi na yaki da talauci, inda ta fatattaki talauci baki daya, shekaru 10 kafin lokacin da MDD ta tsara na ganin bayan talauci.
To a matsayinsu na abokan hulda na kut da kut, tabbas kasashen Afrika ba su da inda za su koyi dabarun raya kansu, ciki har da yaki da talauci, face wajen kasar Sin, saboda gogewa da jajircewarta da kuma yadda ta zama misali ga daukacin duniya.
Jihar Ningxia na daya daga cikin wuraren da Sin ta fafata yaki da takauci inda dukkan kauyukan jihar 1,100 suka yi adabo da talauci. Horon jami’an wanda ya kunshi lakcoci da ziyarce-ziyarce, zai ba su damar gani da idanunsu da tantance irin ayyuka da sadaukarwar da Sin ta yi domin fitar da al’ummarta daga talauci. A ko da yaushe, muna ganin yadda ake alakanta yawan jama’a da gazawar manufofin gwamnatoci na samun sakamakon raya kasa ko yaki da talauci, sai dai, kasar Sin ta nuna cewa, batun ba haka yake ba, wato yawan al’umma ba dalili ne na rashin ci gaba ba. Baya ga haka, kasar Sin ba ta fita ta yi mamaya ko cin zali ko mulkin mallaka ba, kafin kai wa matsayin da ta kai, don haka, babu dalilin cewa rashin karfi ne ya kawo tasgaro ga samun ci gaba. A ganina babban batu shi ne, yadda jami’an nan za su fahimci cewa, kasar Sin dogaro ta yi da mutanenta da ilimi da kwarewarsu da albarkatun da take da shi wajen yakar talauci. Ni ganau ce, domin na je Ningxia, na ga yadda mata suka yaki talauci ta hanyar mayar da ciyawa tsintsiya, da aiwatar da kirkire-kirkire da dama da sauran wasu dabaru. Ba Ningxia kadai ba, dukkan sassan kasar Sin kan yi amfani da duk albarkar da suke da ita wajen mayar ita mai daraja domin kyautata rayuwarsu.
Fatan ita ce, bayan komawa gida wadannan jami’ai su aiwatar da abun da suka koya domin babban kashin bayan ci gaban Sin shi ne, kyakkyawan kudurin shugabanci. (Fa’iza Mustapha)