A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda game da rahoton ci gaban Sin na 2025 da cibiyar nazarin samar da ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, Guo ya ce ci gaban Sin mai inganci ya samar da damammaki ga duniya.
Dangane da furucin Amurka na cewa za ta kara haraji kan katako, da kayan da ake sarrafawa daga gare shi, da ake shigarwa kasar daga ketare, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ba za a samu nasara a yakin ciniki da yakin haraji ba, kuma babu wata hanya ta fita daga ra’ayin ba da kariya ga kasuwa.
Game da shawarar da Amurka ta gabatar ta kawo karshen rikicin Gaza, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin na maraba da goyon bayan duk wani kokari, da zai taimaka wajen ganin an sassauta rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Buku da kari, game da muhawarar babban taron MDD, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ra’ayin kasashen duniya gaba daya, shi ne dole a kiyaye matsayin MDD, da kuma karfafa gudanar da harkokin shugabancin duniya.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp