Cibiyar ilmantar da ‘ya’ya (CGE) ta shirya wa malaman addini da sarakunan gargajiya taron bunkasa ilimin yara mata a arewa da ma Nijeriya gaba daya.
Taron wanda aka gudanar da shi a dakin taro na gidan Sardauna da ke Jihar Kaduna, ya kasance na manyan sarakunan gargajiya da malaman addini kan hanyoyin da za a domin inganta karatun mata tare da nazari da kuma tabbatar da tsarin dabarun rayuwa na cibiyar.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 5 A Kaduna.
- Ɗan Majalisar Wakilai Daga Kaduna Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Da take jawabi a wurin taron, shugabar cibiyar, Hajiya Habiba Mohammed ta bayyana cewa cibiyar tana kokarin inganta rayuwar yara mata masu tasowa a fadin arewacin Nijeriya sama da shekaru 18 da suka gabata.
A cewarta, manufar cibiyar ita ce ta tabbatar da cewa kowace yarinya ba tare da la’akari da asalinta ba, ta samu damar samun ilimi, da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga danginta da kuma al’ummarta.
Hajiya Habiba, ta yi nuni da cewa cibiyar tana aiki da sarakunan gargajiya da malaman addini a arewacin Nijeriya, saboda imani da al’ada, da jagorancin al’umma suna taka rawa wajen tsara rayuwar matasa.