Sama da kashi 90 cikin 100 na ‘yan kasuwa a birnin Yiwu, cibiyar hada-hadar kananan kayayyaki ta kasar Sin, sun amince da biyan kudin kasar Sin na RMB ta hanyar tsarin biyan kudi na zamani na birnin, inda aka bude sama da asusun biyan kudi dubu 60 ta yanar gizo, tare da kulla yarjejeniyar da ta zarce kudin Sin RMB yuan biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 145 da aka yi ciniki ya zuwa yanzu.
Birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake yankin gabashin kasar Sin, ya kaddamar da tsarinsa na gwaji ne, game da tallata tsarin hada-hadar kudi ta yanar gizo na kasar Sin, ko e-CNY a takaice, a kasuwar hada-hadar kananan kayayyaki ta cikin gida. Yana kuma shirin fito da hanyoyi na cin gajiyar tsarin na e-CNY, gami da kasafta tallafin kudi a kananan kasuwannin hada-hadar kayayyaki da biyan albashin ma’aikata, da wurin ajiye motoci, da kudin haya, da na hidimomi. (Mai fassarawa: Ibrahim)