Gomman dalibai sanya da tufafi masu ban sha’awa ne suka buga ganguna tare da rera wake-wake domin murnar sake bude cibiyar koyar da harshen Sinanci da aka yi wa gyaran fuska, a Abuja, babban birnin Nijeriya.
Sashen 18 na kamfanin gine-gine na China Railway ne ya yi wa cibiyar gyaran fuska. An gina cibiyar ne a shekarar 2008, a makarantar karamar sakandare ta yankin Garki Area 11 na birnin Abuja, da nufin kyautata fahimta tsakanin kasashen biyu tun daga matakin farko.
Alhassan Sule, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta birnin tarayya Abuja, ya ce daddadiyar huldar dake tsakanin Nijeriya da Sin, ta taimaka sosai ga hukumar ta samar da ilimin bai daya a birnin.
A cewarsa, masu kula da harkokin bayar da ilimi a yankuna, sun yaba matuka da gyara cibiyar da aka yi, kuma za su ci gaba da tabbatar da ana kula da ita da kayayyakin da aka sanya a ciki, ta yadda dalibai da malamai za su dade suna mora.
A nasa bangaren, jami’in ofishin jakadancin Sin a Nijeriya, Zhang Yi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da mara baya tare da bayar da muhimmanci ga aikin raya makarantu a kasar mafi yawan al’umma a Afrika. (Fa’iza Mustapha)