Bisa labarin da babban bankin jama’ar kasar Sin ya fitar, ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2025, jimillar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje 1,160 ne suka shiga kasuwar hada-hadar lamuni ta kasar Sin, wadanda suka hada da cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasuwanci a kasashe da yankuna fiye da 70, wadanda ke rike da takardun lamuni da yawansu ya kai yuan tiriliyan 4.5, adadin da ya karu da sama da yuan biliyan 270 daga karshen shekarar 2024. Kazalika, jimillar darajar kasuwar lamuni ta kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 183, wanda ke matsayi na biyu a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp